GIDAUNIYAR YAZEED TRUST FUND TA CIYAR DA MARAYU!



Sakamakon samun karin shekara daya daga cikin shekarun da Allah madaukakin sarki da tanadar, matashin Dattijo Alh Yazeed Shehu Danfulani Maidoya Garkuwan Matasan Gusau, kuma Lamidon Tsafe, wannan Gidauniya mai albarka ta  ciyar da Yara Marayu masara galihu a cikin Al'umm, da abinci mai gina jiki, domin kara nuna godiyarsa ga Allah madaukiakin sarki.


Ko shakka babu wannan yana daga cikin godiyar Allah, idan ya maka baiwa ka gode masa, ta hanyoyin da ya tanadar abi wajan yin godiya:

cikin Ikon Allah Gidauniyar Alh Yazeed shehu Danfulani, wato Yazeed Trust Fund karkashin jagorancin hadiminta, Comrade Rufa'i Bala UB salanken Galadima ta shirya gagarumin bikin ciyar da Yara marayu abinci, kyauta hadi da lemo da ruwan sha masu tsafta, domin nuna godiya akan baiwar Allah, wadda yayi masa na kara shekara daya daga cikin shekarun da Allah ya ibar masa a doron Kasa, yara marayu a sassa daban-daban sun ka samu damar halarta wannan ciyarwar, hadi da muhimman mutane da sun ka shedi wannan abin alheri.

Al'umma da dama sun tofa albarkacin bakinsu wajan wannan taron, inda wasu daga cikin sun ka tabo muhimman jawabai, daga ciki akwai, jinjina da bisa wannan namijin kokarin, idan akayi la'akari da babu wani babban mutum ko dan siyasa ko mai hannu da shuni a cikin al'umma wanda ya taba gudanar da wannan aiki, na tawali'u ga marayu da marasa galihu a cikin al'umma.

Ba kasafai ake samu ba a cikin al'umma daukar nauyi hadi da fafutikar ganin an samu cigaba ta kowane fanni a cikin masu dan karamin karfi.

Idan dai masu karatu suna bibiye da mu lokutta da dama mun sha kawo maku abubuwan alheri da gidauniyar Yazeed Trust Fund ke yi a cikin al'umma, dama wannan yana daga cikin tsarin mai Girma Garkuwan Matasan Gusau, wato rungumar Yara masu daraja domin nuna masu cewa ko shakka babu suna da daraja a cikin al'umma, domin idan sun ka tsayu da kafafunsu wata rana za'ayi alfahari da su a cikin al'umma, domin wata rana su ne zasu rike kasar nan.

Babu wata al'umma da take cigaba ko zata cigaba a duniya matukar ba'a rungumi halayyar tausai a cikin al'umma ba, a nan ne sai shugaban wannan Gidauniya ya tabo batun cewa; har yanzu wannan gidauniyar na tsaye wajan daukar nauyin yara marayu zuwa makaranta, da dauke masu wahalhalun karatun, hadi da daukar nauyin rashin lafiyarsu, yace; an tanadi  wani karamin wurin shan magani wanda ake kira da Dansadau inda za'a rika duba marayu marasa lafiya, kyauta, dukkan wadannan suna daga cikin gudunmuwar Alh Yazeed zuwa ga al'umma.

Muna fatan al'umma, 'yan siyasa masu hannu da shuni, 'yan kasuwa da sauran dai-daikun jama'a za su yi koyi da halayyar wannan bawan Allah domin ganin al'umma ta cigaba ta kowane fanni.

Fatan alheri da dukkan masu ruwa da tsaki a cikin tafiyar Alh, Yazeed Shehu Dunfulani, wadanda sunka bada lokacinsu domin hidimtawa ga al'umma.

Daga Nura Mai Apple, Media Reporter daga Gusau.

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’