ZAMU FADADA SHIRINMU NA YAZEED TRUST FUND MATERNITY CARE.......
Garkuwan matasan Gusau,Lamidon Tsafe wato Yazeed shehu Danfulani Mai Doya Gusau,ya jaddadar da ya zabi yaci gaba da zama hadimin al'umma arayuwarsa tare da bayyanar da kudurinsa akan baiwa lafiya fifiko musamman awannan lokaci da rayuwa ta soma tsada ga rayuwar bayin Allah sanadiyar cutar COVID-19.
Lamidon Tsafe Yazeed Shehu Danfulani ya nuna tausayinsa ga yanda al'umma ke samun karancin shigar riba musamman Masu kananan sana'oin hannu,tare da tsaiko akan dakatuwar kasuwancinsu a wajen jahar zamfara(Yan fatauci).
Hakan yasa Yazeed Danfulani yabada Umurnin fadada shirinsa na TAIMAKAWA MATA MASU DAUKE DA JUNA BIYU tare da fadakarwa akan hanyoyin kiyaye Lafiyar juna biyu da matakan dauka ayayin renon juna biyu,tare da bada Magunna Fisabilillah da fatar Allah saukar lafiya.
Allah karfafa yasakama Yazeed da mafificin alhairi.
YAZEED TRUST FUND.
Rufai UB Gusau.
08106580400.
Ameen ya rabbi
ReplyDelete