Talakawa na buƙatar Tallafi
Kasancewar kowace shekara idan irin wannan lokaci ya kama, malamai hadi da dai-dai kun jama'a suna cigaba da kiraye-kiraye domin tallafawa al'umma musamman masu dankaramin karfi. To babu ko shakka, zamu iya cewa kowace shekara akwai sauki sosai idan muka kamanta ta da shakarar bana, domin kuwa ba talakawan ba har masu kudin suna jin a jikinsu, idan muna dubi yadda komai ya tsaya cik sakamakon cutar annobar korona wanda ta addabi duniya baki daya.
Duk da haka, kasancewar sai da ruwan ciki ake janyo na rijiya, akwai bukatar masu hannu da shuni da su dubi girman Allah su taimakawa al'umma, domin ana cikin halin kuncin rayuwa, a bangarori daban-daban na sassan ƙasar nan.
Babu yadda za'ayi mu samu cigaba ta kowane fanni sai in ya kasance mun sanya tausayi ga na kasa damu. Tun cen dama Najeriya tana cikin halin matsi tun kafin zuwan wannan lokaci wanda kuma mafi yawa daga cikin al'ummar ƙasar sun san haka, fatan 'yan uwanmu masu hannu da shuni, 'yan kasuwa da ma'aikatan gwamnati zasu taimakawa al'umma daidai gwargwadon hali, kasancewar wannan wata ne mai matukar tarin lada,
muna roko ga gwamnatocinmu na jihohi musamman wadanda suka kakaba dokar zama a gida domin hanawa tare da dakile yaduwar annobar Korona, su dubi halin da al'umma ke ciki, su fitar da wani kaso na musamman wanda za a rika bi ana tallafawa talakawa na cikin birane da karkara, hakan zai taimaka wajan rage radadin zaman rashi dake addabar al'umma musamman marasa galihu.
Haka muna kira ga gwamnatin tarayyar Najeriya karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari, ya dubi sauran takwarorinsa na wasu kasashe, inda suke bada gagarumar gudunmuwa ga talakawansu, domin rage masu halin da suke ciki na zama a gida, shima ya tallafa ma 'yan kasansa, sannan abi tsari mai kyau wanda tallafi zai iya kaiwa ga wadanda akayi dominsu.
Muna fatan Allah ya kawo mana ƙarshen wannan cuta, kuma ya bada ikon tallafama al'umma, Allah ya karo arziki mai albarka a Najeriya da Afrika da ma duniya baki daya.
Ramadan Mukarram.
Daga Nura Muhammad Mai Apple Gusau 08133376020
Comments
Post a Comment