MEYASA LIKITOCIN NAjERIYA SUKE GUDUWA ZUWA BURTANIYYA?

Daga; Nura Muhammad Mai Apple, Gusau
Ana fama da karancin kwararrun likitoci a Najeriya
Adadin likitocin Najeriya da ke rijistar aiki a Birtaniya ya rubanya cikin shekarar da ta gabata, in ji wani rahoto da kungiyar binciken kwakwaf ta Africa Check ta yi.
Kimanin likitocin Najeriya 12 ne ke rattaba hannu kan yarjejeniyar aiki a Ingila a ko wane mako, in ji binciken.
Yawan likitocin da suka yi karatu a Najeriya kuma suna son aiki a Birtaniya ya karu da kashi 10 cikin 100 cikin shekarar da ta gabata.
Wannan ya rubanya adadin likitocin da ke son yin hakan a shekarar da ta gabata.
Cikin shekara biyar kafin shekarar 2016, kimanin likitocin Najeriya 200 ne ke rijistar aiki da hukumar kula da aikin kiwon lafiya ta Birtaniya a kowace shekara.
Amma a bara adadin likitocin Najeriyar da suka yi rijistar aiki a Birtaniyar ya kai 439.
‘Yan Najeriya kamar wanda ke kwance a wannan hoton na fita kasashen waje irin su Indiya saboda rashin ingantaccen tsarin kiwon lafiya a kasar
Babu tabbacin abin da ya sa yawan likitocin da ke son aiki a Birtaniya ya karu sosai cikin kankanin lokaci.
Najeriya dai tana fama da karancin ma’aikatan kiwon lafiya inda majinyata ke yiwa likitoci yawa a asibitocin gwamnati.
Likitocin dai na korafiun rashin kayan aiki da kuma kulawa mai kyau, kuma wasu na ganin hakan na daga dalilan da suka sa wsu ke bguduwa daga kasar.
TAHOTO DAGA NURA MUHAMMAD MAI APPLE GUSAU

Comments
Post a Comment