Masana sun ce daga cikin abubuwan da suka sa dan Adam yin galaba a kan sauran halittu shi ne yadda yake iya hada kai. Don mutum shi kadai ba zai iya gwada karfi da zaki ko giwa ba. Amma idan ya hada karfi da sauran ‘yan uwansa babu kalubalen da ba za su iya tinkara ba. Hadin kai kuma ba ya tabbata sai da yarda, kuma yarda sai da mu’amala. Masu hikimar magana sun ce, Allah Ya halicce mu da kunne biyu, ido biyu amma sai ya yi mu da baki daya domin mu kalla, mu kuma saurara fiye da yadda muke magana. Amma sai ya kasance cewa mun fi son yin magana fiye da saurare. Sau da yawa idan muna tattaunawa da wadansu ba ma mayar da hankali kan abin da ake fadi. Kawai jira muke mutum ya kai aya - idan ba mu katse shi ba kenan, domin mu fadi namu ra’ayin. Ga shi kuma ba mu son jin ra’ayoyin da suka sha bamban da namu. To ina za a samu fahimtar juna har a yi aiki tare? Babu wanda rayuwarsa iri ɗaya da ta wani, kowa da irin jarabawar shi, kowa kuma da irin ta shi f...
Kungiyar ta gindayawa shugaban kasa sharadi da cewar, in har yana son goyon bayan su a zaben 2019 to sai ya sauya kujerar da mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo yake kai a yanzu da wani dan kabilar su na yankin Kudu maso Gabashin kasar nan Majiyarmu ta fahimci wannan sharadi ya zo ne bayan da shugaba Buhari ya yanke shawarar ziyartar jihohin Kudu maso gabashin kasar a makonnin da suka gabata. A wani rahoto da sanadin shugaban kungiyar Chilos Godsent da ya bayyana a birnin Owerri na jihar Imo, ya ce wannan ita kadai ce hanyar da jam’iyyar APC za ta samu goyon bayan su a zaben kasa na 2019. Godsent ya kara da cewa, jam’iyyar APC ta maishe da yankin na su saniyar ware wajen gudanar da shugabancin ta a kasar.
A Najeriya, yayin da ake ci gaba da cece-kuce game da dokar hana kiwo da ta soma aiki a jihar Benue da ke arewa ta tsakiyar kasar, ministan noma da raya karkara na kasar Audu Ogbeh, ya shaida wa BBC cewa saboda rikicin da ake yawan samu tsakanin manoma da makiyaya, dole ne a kintsa makiyayan wuri guda, sannan za’a samar da wurare na musamman domin shanu inda za’a basu ciyawa da ruwa mai kyau. Ministan ya ce, idan har aka yi hakan, to su kansu makiyayan ba za su so su yi yawo ba, kuma ko ba komai an kare su daga barazanar masu satar shanu. Dangane da batun kafa dokar hana kiwo a jihar Benue, ministan ya ce matsin lambar mutane ne ya tilasta wa gwamnan jihar kafa wannan doka saboda tashe-tashen hankulan da ake samu tsakanin manoma da makiyaya a jihar. Mr Audu Ogbeh, ya ce nan ba da jimawa ba za’a fara aiki a wuraren kiwo na musamman da aka kebe, na farko a jihar Kano, sai kuma na jihar Neja. Ya ce da sannu a hankali mutane za su fahimci cewa lallai ana bukatar naman shan...
Masha Allah
ReplyDelete