HALAYYAR KIRKI SABO! Daga majalisar Himma Shayi.
Yana daga cikin cikar kamilin ɗan Adam cika alƙawari, yunkurin Gidauniyar (Alh, Yazeed Shehu Ɗanfulani Mai Doya), wajan ganin al'umma sun samu na kansu. Wannan Gidauniya ta samu damar komawa a majalisar Himma Shayi, domin cika alƙawarin da ta ɗauka a siyan sabon injinin yin faci sabo fin ga shugaban wannan ƙungiya ta majalisar himma, dake a mazauni wajan gidan man mai Littafai dake daura da kasuwar kanawa a nan cikin Tudan wada, Gusau babban birnin jihar Zamfara.
Idan dai masu karatu suna biye da mu a cikin wannan makon ne mai ƙarewa wannan Gidauniya ta samu zuwa wannan majalisa ta Himma shayi, in da ta ƙaddamar da Forms ga (Yara Masu Daraja) marayu da kuma marasa galihu a cikin al'umma, 20 da zimmar daukar nauyinsu zuwa makaranta, don bayar da tashi gudunmuwa ta fuskar ilimi abun nema!
A lokacin da gidauniyar Yazeed Trust Fund ta ziyarci majalisar Himma shayi wajan ƙaddamar da wannan forms ta lura sosai shugaban majalisar wanda kuma shine mai yin sana'r Faci a wajan, injinin da yake amfani da shi wajan daukar nauyin iyalansa ya tsufa sosai, wanda hakan kan kawo masa cikas wajan neman abun sawa ga bakin salati. Gidauniyar ta lashi takobin kawo masa sabon injin domin yayi amfani da shi wajan daukar ɗawainiyar iyalinsa.
A cikin jawabin limamin tafiyar Gidauniyar (Alh Yazeed Shehu Ɗanfulani Mai Doya Garkuwan Matasan Gusau, Lamiɗon Tsafe) wato (Comrade Rufa'i Bala UB Salanken Galadima) ya taɓo muhimman abubuwa inda da farko ya fara sallama sannan ya ci gaba da jawabinsa kamar haka; "Alhamdulillahi a bisa alƙawarin da mu kayi na bayar da wannan tallafi a wannan majalisa ba muyi ƙasa a gwiwa ba, mun zo domin cika wannan alƙawari, ga wannan shugaban majalisa a matsayin yana uba dattijo kuma shugaba a wannan majalisa sama da shekaru 20 da suka gabata, kuma wannan majalisa ba'a taɓa kamata da wani laifi ba a hukumance, majalisa ce wadda ta tara al'umma mabambanta kamar 'yan siyasa, jinin sarauta, dattijai, matasa, da sauran al'umma".
"saboda haka mun ka dawo wannan majalisar domin cika wannan alƙawari da muka dauka, kasancewar muna da damar yin haka. saboda haka cike da fatan wannan Genaretor da muka damƙa maka, Allah ya sanya albarka da alheri a ciki, ya sa nan da shekara mai zuwa kaima ka baiwa wani".
A ƙarshe ya godewa wannan majalisar da kuma al'ummar da wannan majalisa ta tara, a bisa wannan gagarumar tarbo da aka samu daga wannan waje, tun daga karramawa da shayi na gaske, da kuma shimfiɗar fuska.
Haka a lokacin da aka bayar da turun magana ga shugaban majalisar ya nuna matuƙar farin cikinsa a bisa wannan namijin ƙoƙari, na bashi wannan abun neman abinci, sannan yayi kira ga sauran 'yan siyasa da masu hannu da shuni da suyi ko'i da halayyar Yazeed wajan taimakon al'umma gwargwadon hali. A ƙarshe yayi addu'ar Allah ya saka masa da mafificin alhari.
A lokacin bayar da wannan kyauta na lura sosai, da bayanai da wani jigo daga cikin dattawan majalisar yayi na cewa, basu da abinda zasu iya cewa ga Yazeed sai dai fatan alheri, domin ya yi masu halacci da karamci a lokacin suka isa jihar Kaduna wajan gudanar da wasu ayyuka, Allah ya ƙaddara sun kayi kicibis da wajan saukar baƙi na (Alh Yazeed Shehu Ɗanfulani) a jihar Kaduna, duk da kasancewar su basu san wannan waje na ɗan Zamfara ne ba, amma da Yazeed yaji ance 'yan Zamfara ne, nan take aka shigar da su wannan waje, kuma suka zauna a ciki, har tsawun lokaci da sun ka buƙaci komawa gida. Yace wani babban abun burgewa shine irin yadda wajan an rarraba shi ɓangare-ɓangare kuma an rubuta sunayen wasu daga cikin sunayen sassan jihar Zamfara.
Bayan kammala nashi jawabin wasu da dama sun gabatar da nasu jawaban, daga karshe sunyi addu'a da fatan alheri ga wannan tafiya mai cike da alheri.
Daga yanzu Kowane lokaci, al'ummar majalisar Himma Shayi A Shirye Suke su bada tasu gudunmuwa, idan buƙatar hakan ta samu!
Daga Nura Mai Apple Media Reporter.
Comments
Post a Comment