Skip to main content

MATAKAN DA SHUGABAN KASAR CHADI YA DAUKA SUN DACE!





Fannin samar da tsari, walwala hadi da jin dadin al'umma, wannan babban nauyi wanda ya rataya a wuyan kowane shugaba halatacce, wanda al'umma sun ka zaɓa da zimmar inganta rayuwarsu ta fannoni da dama. Demokaradiyya a siyasance tsari ne wanda aka fito da shi domin shugabannin duniya su saki mara ga talakawansu, su samar masu da kayayyakin more rayuwa, kama tun daga, inganta tsaro, wadata kasa da abinci, samar da hanyoyi, samar da wutar lantarki, samar da ilimi, samar da ruwan sha, da kuma fannin lafiya._
_Babu wata kasa a duniya da zata ci gaba matukar babu waɗannan. Babban abun nema ruwa-ajallo shi ne; tsaro, domin sai da shine sannan komai zai gudana cikin jin dadi da walwala.


Mun ya ba matuƙa ga irin yadda shugaban kasar Chadi Idris Daby yake kokarin ganin ya tsame kasarsa daga cikin jerin kasashen dake fama da safgar ta'addanci, ko shakka babu wannan shugaba yayi abun yabawa idan mukayi la'akari da yadda shugaban ya zage damtse, an ka fita da shi filin daga domin yaki da 'yan ta'adda waɗanda sun ka zama ƙarfen ƙafa a cikin yankunan ƙasashen dake kewaye da tafkin Chadi.


Wannan nasara da zaratan sojojin kasarsa suka samu abin murna ne, kuma hakan wata manuniya ce dake nuna shugaban kasar da gaske yake wajan fito-na-fito da 'yan kungiyar mayakan Boko Haram, masu kokarin ganin sun kassara waɗannan kasashe namu masu albarka.


Kan abin da ya shafi wannan yaki, ko shakka babu bai kamata abar shugaban kasar Chadi da wannan gumurzo shi kaɗai ba, akwai buƙatar kasashen Najeriya da Nijar da Kamaru su taimaka masa, domin ganin an samu nasarar wannan yaki, kasancewar dukkan wadannan kasashen suna fama da matsalolin tsaro haiƙan!


Idan sauran kasashen da ke kewaye da wannan yanki sun ka fito kamar yadda Shugaba Idris Daby ya fito an kayi hadaka ta musamman wadda ba sani ba sabo, insha Allahu da karfin Allah za'a samu nasarar kawo karshen wannan al'amari wanda yasa da yawa daga cikin dubban mutane sun ka rasa rayukansu, wasu da dama sun ka rasa muhallansu, da dama daga cikin wasu sun ka rasa abin da zasu ci ta sanadiyar wannan kalubale, shekaru da dama da suka gabata.


Faɗa irin wannan mai cike da hatsari akwai buƙatar a cire son zuciya a haɗu a bisa manufa daya, domin samun nasara, kasancewar yaƙi ɗan zamba ne, kowace ƙasa akwai irin nata gudunmuwar da zata iya bayarwa ta fuskoki da dama.


Kalaman shugaban kasar ta Chadi da ya furta na cewar dakarun Ƙasarsa, ba zasu kara fita kasar ba, da zimmar taimakon wata kasa, sai dai su tsaya su tsare Ƙasar ta su, domin ganin sun kakkaɓe kasar daga ƙangi na tsaro, ƙura ce ta kai bango, to sai dai kuma wannan wata manuniya ce ga kasashen da wannan lamari ya shafa. Muna fatan dai zai mayar da wuƙarsa kube, ya samu haɗin kan sauran kasashen yankin dake keyawa da Tafkin na Chadi, don haɗa gwiwa domin ganin an samu kaiwa ga nasara.

A karshe muna addu'ar Allah ya kawo mana karshen wannan lamari da ya daɗe yana ciwa al'umma tuwo a kwarya, Allah ya kawo mana lafiya da zama lafiya da arziki mai albarka a kasashenmu na Afrika dama duniya baki daya, zaman lafiya ya fi zama dan sarki. Nagode!


Daga Nura Mai Apple,  Shugaban Ƙungiyar Matasa 'Yan Gwagwarmaya.




Copyright©maiapple

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Masana sun ce daga cikin abubuwan da suka sa dan Adam yin galaba a kan sauran halittu shi ne yadda yake iya hada kai. Don mutum shi kadai ba zai iya gwada karfi da zaki ko giwa ba. Amma idan ya hada karfi da sauran ‘yan uwansa babu kalubalen da ba za su iya tinkara ba. Hadin kai kuma ba ya tabbata sai da yarda, kuma yarda sai da mu’amala. Masu hikimar magana sun ce, Allah Ya halicce mu da kunne biyu, ido biyu amma sai ya yi mu da baki daya domin mu kalla, mu kuma saurara fiye da yadda muke magana.  Amma sai ya kasance cewa mun fi son yin magana fiye da saurare. Sau da yawa idan muna tattaunawa da wadansu ba ma mayar da hankali kan abin da ake fadi. Kawai jira muke mutum ya kai aya - idan ba mu katse shi ba kenan, domin mu fadi namu ra’ayin. Ga shi kuma ba mu son jin ra’ayoyin da suka sha bamban da namu. To ina za a samu fahimtar juna har a yi aiki tare?  Babu wanda rayuwarsa iri ɗaya da ta wani, kowa da irin  jarabawar shi,  kowa kuma da irin ta shi f...

LABOUR ROOM BLOBAL INITIATIVE KIRA NA MUSAMMAN ZUWA GA MATASA DA 'YAN SIYASA

Duk tarin dukiyarka, ko girman mulkinka ko zamanka basarake, ba zaka taɓa jin daɗin abinda kake taƙama da shi ba, matuƙar al`ummar da kake rayuwa a cikinta ba su zaune lafiya ko da kai ka tsira, kuwa. Shi dama talaka juji ne, duk wani tarin dattin tashin hankali, akansa yake ƙarewa. Da shi ake amfani wajen tashe-tashen hankula, shi ke kisa kuma shi ake kashewa kuma duk masifar da kan biyo baya a kansa ne take sauka. In ko haka ne, haƙiƙa da sake! kenan kowa na matuƙar kaunar zaman lafiya a cikin al'umma, domin sai da zaman lafiya ɗin ne, kowa zai iya morewa, har ya iya rayuwarsa ba tare da shiga tasko ba. A kan haka ne! Ƙungiyar Labour Room Global Initiative haɗin gwiwa da Ƙungiyoyin Jihar Zamfara ke amfani da wannan damar wajan kira ga dukkanin 'yan Siyasa, da ayi siyasa ba tare da gaba ba. Domin in dai har za'a iya zubar da jini a kashe rai a zaɓen fitar da gwani kurrum na jam'iyya ɗaya, to ina ga zaɓen gama-gari da ke tafe? Don haka muna amfani da wannan ...

MUNA JIMAMIN RASHIN 'YAR ADU'A

hakika tarihi ba zai taba mantawa da tsohon shugaban Kasar Najeriya ba, margayi Alh Umar Musa 'yar Adu'a, kasancewarsa duk da baiyi wani dadewa ba a kan karagar jagorancin kasar nan, amma Najeriya ta shedi gwagwarmayarsa, ta fannoni da dama. Idan muka yi la'akari da yadda ya zage damtse wajan fafutikar ganin Najeriya ta zauna lafiya, musamman rikice-rikicen 'yan tawayen Niger-Delta da sauransu. Idan muka dubi fannin samar da ilimi wanda a nan sashen yayi rawar gani, haka a fannin kiyon lafiya da cigaban rayuwa. Lokacin Alh Umar Musa 'yar'adua yana shugaban kasa talakawa da dama sun dara, kasancewar yayi yunkurin ganin kasar nan ta samu cigaba ta kowane fanni. Muna fatan Allah yaji kanshi ya masa rahama ya sanya aljanna ta kasance makoma a gareshi. Najeriya tayi babban rashi. Daga Nura Muhammad Mai Apple Gusau 08133376020