_KUNGIYAR MURYAR TALAKA ZA TA KARRAMA GWARZAYEN SHEKARA:_*
Duk Shekarar Kungiyar Muryar Talaka Reshen Jahar Zamfara ta kan zabi wasu Muhimman mutane Tana KARRAMA su. , akan wasu Muhimman gudunmuwowi da sunka bayar wajen cigaban al'umma a bangarensu! A lokacin Babban taron kungiyar na Shekara-shekara. Sai dai a wannan Shekarar shirin zai dan sauya sabon salo. A wannan Shekarar za mu Kalli jagororinmu ne, tun daga Kansiloli, shuwagabannin kananan hukumomi, 'yan Majalissar Dokokin na jaha, 'Yan Majalissar wakilai na tarayya da kuma 'yan Majalissar dattawa na tarayyarmu. Inda kowane bangare cikinsu za ku zabi daya da ya zama zakara wajen kyautatawa al'ummarsa, mu kuma mu karrama shi. Haka zalika za mu zabo wasu Muhimman mutane zuwa biyar da za mu fitar cikinsu ku zabi daya, a matsayin gwarzon SHEKARA. Ga ranakun da zaben zai Gudana. 1.kansiloli 1/1/2018 to 3/1/2018 2.ciyamomi 4/1/2018 to 6/1/2018 3. State House Assembly 7/1/2018 to 9/1/2018 4.National Assembly 10/1/2018 to 12/1/2018 5.Senators 13/1/2018 t...