Ban Taba Ganawa Da Buhari Ba, Jibrin Ya Mayar Da Martani Ga Dogara



Tsohon ciyaman na kwamitin ‘yan majalisar wakilai akan kasafin kudin kasa, Abdulmumin Jibrin, ya bayyana cewa shugaba Buhari bai taba tuntubar sa ba akan tuhumar da yake yiwa shugaban majalisar wakilai, Honorabul Yakubu Dogara, da cewar ya kulla wata makekashiya a cikin kasafin kudi na shekarar 2016.

NAIJ.com ta fahimci cewa, Jibrin ya tuhumi shugaban na majalisar wakilai da kulla wata makekashiya akan kasafin kudi na shekarar 2016 da suka tasar ma Naira miliyan 284.

A cikin wani rubutaccen littafi na tarihin rayuwar Dogara wanda Dele Momodu ya wallafa, shugaban na majalisar wakilai ya bayyana cewa, Buhari ya gargadi Honorabul Jibrin akan kar ya sake tunkarar sa da wannan lamari.

A kalaman Dogara, “Kasancewar shugaba Buhari mai tsari da hangen nesa, ya bukaci masaniya ta inda sauran shugabannin majalisar wakilai suka shiga a yayin da shugabanni hudu suka kebance wajen yin surkulle akan kasafin kudin.”

“Babu ko mutum guda dake yi mana wannan fassara da zasu iya bayar da amsar wannan tambaya. Tun da dai kowa yana da idanu na basira, matukar babu amsa ta wannan tambayar to baya bukatar a sake tunkarar sa da wannan batu.”

KARANTA KUMA: Siyasar 2019: Atiku ya fara tuntubar gwamnoni da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP

A yayin mayar da martani akan batutuwan Dogara da Jibrin yayi a ranar Larabar da ta gabata ya bayyana cewa, akwai rubutattun wasiku har guda uku da ya aikawa shugaban kasa, sai dai babu ko guda da ya samu amsar ta.

Ya kara da cewa, ya fahimci cewa akwai wani shinge da Dogara ya gindaya masa a tsakanin sa da shugaba Buhari, saboda haka ya ci gaba da fafutikar bayyanar da gaskiya a karan kan sa, ya kuma dakatar da kokarin sa na neman ganawa da shugaba kasa.

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’