Janar Ibrahim Babangida Ya Yi Wa Jam’iyyar PDP Fatan Alheri
Tsohon shugaban Najeriya na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida IBB, ya yi wa jam’iyyar adawa ta PDP fatan alheri yayin da take kokarin shirya babban taronta na kasa inda za ta zabi sabbin shugabanninta a karshen wannan mako.
A cewar tsohon shugaba Ibrahim Badamasi Babangida hankalinsa na wurin taron kasa da jam’yyar PDP ke shirin gudanarwa ranar wannan Asabar mai zuwa. Fatansa shi ne a kammala taron lafiya.
Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya kira taron manema labarai ne a Minna domin yiwa dubban ‘yan kasuwar tsohuwar Panteka dake Kaduna da suka tafka asarar miliyoyin Nera sakamakon gobarar da ta lakume kasuwar, lokacin ne ya yi furucinsa akan PDP.
Tsohon shugaban yana fatan ‘yan jam’iyyar zasu kai zuciya nesa a taronsu tare da rungumar kaddarar shan kaye. Yana cewa “Na yi masu kyakyawan fata. Ina son duk yadda za’a yi… tunda siyasa ake, wasu su ci, wasu ba zasu ci ba. Wanda ya ci ya dauka haka Allah ya yi. Sun ci kuma aiki ne na jama’a”.
A cewar tsohon shugaban muddin wadanda aka zaba sun yiwa jama’a aiki bukata ta biya tare da kara fatan Allah ya sa su yi taro lafiya su kuma tashi lafiya.
Janar Babangida ya na da ra’ayin cewa yin adalci ga sabbin shugabannin da za’a zaba su karbi shugabancin jam’iyyar ya na da matukar tasiri wajen tunkarar babban zabe mai zuwa. Ya ce a matsayinsu na shugabannin kamata ya yi jam’iyyar ta nemi shugabanni masu adalci, masu gaskiya, masu fasaha da suka amince da siyasa. Sun san kanta kuma zasu taimakawa magoya bayansu.
Dangane da komawar Alhaji Atiku Abubakar jam’iyyar PDP, Janar Babangida ya ce tsarin mulkin kasa ya bashi hurumin yin hakan tare da iya shiga kowace jam’iyya.
Kawo yanzu mutane takwas ne ke neman kujerar shugabancin jam’iyyar ta PDP.
Comments
Post a Comment