Skip to main content

Uche Secondus Ya Zama Sabon Shugaban Jam’iyyar PDP



An zabi Uche Secondus a matsayin sabon shugaban babbar jam’iyyar adawa a Najeriya, PDP, bayan da aka kammala kidaya kuri’un zaben da aka gudanar jiya Asabar.

Tsohon mukaddashin shugaban jam’iyyar PDP Prince Uche Secondus ne ya lashe zaben shugabancin jam’iyyar bayan kammala babban taron jam’iyyar da ya kawo karshen kwamitin riko na Sanata Ahmed Makarfi.

Secondus daga yankin kudu maso kudancin Najeriya, ya samu kuri’u 2000 inda ya yi nasara kan abokan takarar sa biyu Farfesa Tunde Adeniran da Chief Raymond Dokpesi.

Tun gabanin taron, wassu daga wadanda su ka aiyana tsayawa takarar da su ka hada da Bode George da Gbenga Daniel sun janye; inda har George ke zargin cewa gwamnan Rivers Nyesom Wike ya nunawa Yarbawa wariya musamman don mara baya ga Secondus.

Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar daTom Ikimi da sauran gwamnonin jam’iyyar irin su Ayo Fayose da Ibrahim Dankwambo sun shaida sanarda sakamakon da a ka yi daidai karfe uku da minti goma sha biyar na safe agogon Najeriya.

Yanzu jam’iyyar za ta tura tikitin takarar shugaban kasa yankin arewa a shekarar 2019.

Alamu na nuna har yanzu gwamnoni na da tasirin juya lamurra a manyan jam’iyyun Najeriya.

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Masana sun ce daga cikin abubuwan da suka sa dan Adam yin galaba a kan sauran halittu shi ne yadda yake iya hada kai. Don mutum shi kadai ba zai iya gwada karfi da zaki ko giwa ba. Amma idan ya hada karfi da sauran ‘yan uwansa babu kalubalen da ba za su iya tinkara ba. Hadin kai kuma ba ya tabbata sai da yarda, kuma yarda sai da mu’amala. Masu hikimar magana sun ce, Allah Ya halicce mu da kunne biyu, ido biyu amma sai ya yi mu da baki daya domin mu kalla, mu kuma saurara fiye da yadda muke magana.  Amma sai ya kasance cewa mun fi son yin magana fiye da saurare. Sau da yawa idan muna tattaunawa da wadansu ba ma mayar da hankali kan abin da ake fadi. Kawai jira muke mutum ya kai aya - idan ba mu katse shi ba kenan, domin mu fadi namu ra’ayin. Ga shi kuma ba mu son jin ra’ayoyin da suka sha bamban da namu. To ina za a samu fahimtar juna har a yi aiki tare?  Babu wanda rayuwarsa iri ɗaya da ta wani, kowa da irin  jarabawar shi,  kowa kuma da irin ta shi f...

LABOUR ROOM BLOBAL INITIATIVE KIRA NA MUSAMMAN ZUWA GA MATASA DA 'YAN SIYASA

Duk tarin dukiyarka, ko girman mulkinka ko zamanka basarake, ba zaka taɓa jin daɗin abinda kake taƙama da shi ba, matuƙar al`ummar da kake rayuwa a cikinta ba su zaune lafiya ko da kai ka tsira, kuwa. Shi dama talaka juji ne, duk wani tarin dattin tashin hankali, akansa yake ƙarewa. Da shi ake amfani wajen tashe-tashen hankula, shi ke kisa kuma shi ake kashewa kuma duk masifar da kan biyo baya a kansa ne take sauka. In ko haka ne, haƙiƙa da sake! kenan kowa na matuƙar kaunar zaman lafiya a cikin al'umma, domin sai da zaman lafiya ɗin ne, kowa zai iya morewa, har ya iya rayuwarsa ba tare da shiga tasko ba. A kan haka ne! Ƙungiyar Labour Room Global Initiative haɗin gwiwa da Ƙungiyoyin Jihar Zamfara ke amfani da wannan damar wajan kira ga dukkanin 'yan Siyasa, da ayi siyasa ba tare da gaba ba. Domin in dai har za'a iya zubar da jini a kashe rai a zaɓen fitar da gwani kurrum na jam'iyya ɗaya, to ina ga zaɓen gama-gari da ke tafe? Don haka muna amfani da wannan ...

MUNA JIMAMIN RASHIN 'YAR ADU'A

hakika tarihi ba zai taba mantawa da tsohon shugaban Kasar Najeriya ba, margayi Alh Umar Musa 'yar Adu'a, kasancewarsa duk da baiyi wani dadewa ba a kan karagar jagorancin kasar nan, amma Najeriya ta shedi gwagwarmayarsa, ta fannoni da dama. Idan muka yi la'akari da yadda ya zage damtse wajan fafutikar ganin Najeriya ta zauna lafiya, musamman rikice-rikicen 'yan tawayen Niger-Delta da sauransu. Idan muka dubi fannin samar da ilimi wanda a nan sashen yayi rawar gani, haka a fannin kiyon lafiya da cigaban rayuwa. Lokacin Alh Umar Musa 'yar'adua yana shugaban kasa talakawa da dama sun dara, kasancewar yayi yunkurin ganin kasar nan ta samu cigaba ta kowane fanni. Muna fatan Allah yaji kanshi ya masa rahama ya sanya aljanna ta kasance makoma a gareshi. Najeriya tayi babban rashi. Daga Nura Muhammad Mai Apple Gusau 08133376020