Skip to main content

_KUNGIYAR MURYAR TALAKA ZA TA KARRAMA GWARZAYEN SHEKARA:_*



Duk Shekarar Kungiyar Muryar Talaka Reshen Jahar Zamfara ta kan zabi wasu Muhimman mutane Tana KARRAMA su. , akan wasu Muhimman gudunmuwowi da sunka bayar wajen cigaban al'umma a bangarensu! A lokacin Babban taron kungiyar na Shekara-shekara.

Sai dai a wannan Shekarar shirin zai dan sauya sabon salo.

A wannan Shekarar za mu Kalli jagororinmu ne, tun daga Kansiloli, shuwagabannin kananan hukumomi, 'yan Majalissar Dokokin na jaha, 'Yan Majalissar wakilai na tarayya da kuma 'yan Majalissar dattawa na tarayyarmu. Inda kowane bangare cikinsu za ku zabi daya da ya zama zakara wajen kyautatawa al'ummarsa, mu kuma mu karrama shi.

Haka zalika za mu zabo wasu Muhimman mutane zuwa biyar da za mu fitar cikinsu ku zabi daya, a matsayin gwarzon SHEKARA.

Ga ranakun da zaben zai Gudana.

1.kansiloli 1/1/2018 to 3/1/2018

2.ciyamomi 4/1/2018 to 6/1/2018

3. State House Assembly  7/1/2018 to 9/1/2018

4.National Assembly 10/1/2018 to 12/1/2018

5.Senators 13/1/2018 to 15/1 /2018

6. Gwarzon shekara 16/1 /2018 to 20/1 /2018

7.Tattara sakamakon 20/1 /2018 to 25/1 /2018

8.Fadin sakamako 28/1 /2018

A yayin zaben za mu sanar da ku dokoki da ka'idojin zaben GWARZAYEN SHEKARA NA MURYAR TALAKA!

Sign: PRO I

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Masana sun ce daga cikin abubuwan da suka sa dan Adam yin galaba a kan sauran halittu shi ne yadda yake iya hada kai. Don mutum shi kadai ba zai iya gwada karfi da zaki ko giwa ba. Amma idan ya hada karfi da sauran ‘yan uwansa babu kalubalen da ba za su iya tinkara ba. Hadin kai kuma ba ya tabbata sai da yarda, kuma yarda sai da mu’amala. Masu hikimar magana sun ce, Allah Ya halicce mu da kunne biyu, ido biyu amma sai ya yi mu da baki daya domin mu kalla, mu kuma saurara fiye da yadda muke magana.  Amma sai ya kasance cewa mun fi son yin magana fiye da saurare. Sau da yawa idan muna tattaunawa da wadansu ba ma mayar da hankali kan abin da ake fadi. Kawai jira muke mutum ya kai aya - idan ba mu katse shi ba kenan, domin mu fadi namu ra’ayin. Ga shi kuma ba mu son jin ra’ayoyin da suka sha bamban da namu. To ina za a samu fahimtar juna har a yi aiki tare?  Babu wanda rayuwarsa iri ɗaya da ta wani, kowa da irin  jarabawar shi,  kowa kuma da irin ta shi f...

Pakistani Campaigner for the ‘Disappeared’ Himself Goes Missing Four Activists Feared Forcibly Disappeared in Sindh Province

Pakistani Campaigner for the ‘Disappeared’ Himself Goes Missing Four Activists Feared Forcibly Disappeared in Sindh Province Saroop Ijaz It was only last month when Punhal Sario marched from the Pakistani cities of Hyderabad to Karachi to demand the return of fellow activists who had gone “missing,” a Pakistani euphemism for those forcibly disappeared by the state authorities. Now, Sario himself is feared missing . Witnesses say that Sario, a 58-year-old human rights activist and head of the Voice for Missing Persons of Sindh, was abducted from Hyderabad by security forces on August 3. Four days later, men in plainclothes accompanied by police officials abducted three other people – Partab Shivani, a teacher and activist; Naseer Kumbhar, a writer; and Mohammad Umer, a political party worker – from the Tharparkar district of Sindh province. Pakistani authorities deny any involvement, but have produced no information on the men’s whereabouts. In a further show of intimidation of cri...

KUNGIYAR MURYAR TALAKA TA BAYAR DA TALLAFIN KAYAN MAKARANTA, GA DALIBBAI DA KADDAMAR DA SHUWAGABANNINTA A KARAMAR HUKUMAR MARU!

A yau Talata 19-12-2017 kungiyar Muryar Talaka ta kasa Reshen Jahar Zamfara. Kai ziyara a Karamar hukumar Maru domin bayar da tallafin kayan karatu ga dalibbai a makarantun Gwamnati da ke wadannan karamar hukumar . A lokacin ziyarar wadda shugaban kungiyar na Jahar Zamfara, Comrade HAFIZU BALARABE GUSAU. ya jagoranta. Ya bayyana cewa, kungiyar Muryar Talaka ta bullo da wannan shirin ne, domin tallafawa, wajen cigaban bangaren ilimi a wannan jahar. Wanda hakan ne, ya sa kungiyar ta bullo da wannan shirin La'akkari da yadda wasu uwaye su ke da matukar rauni wajen daukar nauyin dawainiyar 'ya'yansu. Haka zalika hakan zai taimaka wajen habbaka sha'anin ILIMI a Jahar Zamfara. A lokacin da ya ke jawabi shugaban makarantar BANAGA SULE Primary school, Maru. Ya bayyana kungiyar muryar Talaka da cewa "Kungiya ce da ya kamata sauran kungiyoyi su yi koyi da ita. "Dan Haka ya kamata ku Kara jajircewa wajen aiki tukuru. Musamman ganin cewa kungiyar, ba kungiya ba ...