Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari Ya Ziyarci Gidan Kurkuku A Kano Domin Ganin Halin Da Fursunoni Ke Ciki
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa jihar Kano bisa ziyarar aiki na kwanaki biyu kamar yadda fadar shugaban kasa ta tabbatar a yau Laraba, 6 ga watan Disamba.
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya ziyarci gidan kurkuku a Kano domin ganin halin da fursunoni ke ciki
A lokacin da shugaban kasar ya isa Kano, kai tsaye ya tafi fadar sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II inda ya kwashi gaisuwa.
Daga nan kuma ya ziyarci gidan kurkuku na Kurmawa dake jihar. Daya daga cikin kakakin sa, Bashir Ahmad, yace shugaban kasar ya kai ziyarar ne domin ya ga halin da fursunonin ke ciki.
Sannan kuma shugaban kasar ya kaddamar da sakin fursunoni 500 wanda gwamnatin Kano ta yi ma gafara a kurkukun na Kurmawa.
Comments
Post a Comment