Jam’Iyyun Adawar Najeriya Na Kokarin Yiwa APC Taron-Dangi



Mun ji cewa wata Jam’iyya a Najeriya mai suna PPP na shirin doke Jam’iyyar APC mai mulki a zabe mai zuwa na 2019. Jam’iyyar tace amma fa kifar da Gwamnati mai ci a Kasar sai an yi da gaske.

Jam’iyyar PPP tuni ta fara hangen zaben 2019 inda tace za ta nemi goyon bayan sauran Jam’iyyun adawa na kasar da su yi taron-gwiwa domin yin waje da APC. Kamar yadda mu ka samu labari Shugaban Jam’yyar ya bayyana wannan.

Damian Ogbonna wanda shi ne Shugaban Jam’iyyar na PPP na kasa yace babu Jam’iyyar da ta isa ta kada Gwamnati mai ci ita kadai . Don haka ne yace dole ayi kokarin hada karfi-da-karfe domin ganin an iya doke Jam’iyyar da ke mulki 2019.

Jam’iyyar ta na kokarin tuntubar sauran Jam’iyyun adawan kasar irin su PRP da CAA domin ganin an ba APC kashi. Ogbonna ya kuma nemi Jama’a su yi kokarin fita zabe mai zuwa domin ko da yana ganin har yanzu ana tafka magudin zabe.

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’