Gwamnatin Tarayya Ta Bawa David Mark Wa’Adin Kwanaki 21 Ya Tattara Nasa-Ya-Nasa Ya Fice Daga Gidan Shugaban Majalisar Dattijai
Gwamnatin tarayya ta zargi tsohon shugaban majalisar dattijai, David Mark, da mallakar gidan shugaban majalisar ta haramtacciyar hanya.
Kwamitin bincike da kwato kadarorin gwamnatin tarayya da ofishin shugaban kasa ya kafa a watan Satumba karkashin jagorancin Cif Okoi Obono-Obla ya gano hakan kuma ya dibawa Mark wa’adin kwanaki 21 ya tattara nasa ya nasa ya bar gidan.
Tsohon Shugaban Majalisar Dattijai David Mark
A cikin takardar wa’adin kwanakin barin gidan da kwamitin ya aikewa Mark, an bukaci da ya gabatar da wata hujja, idan yana da ita, da zata hana gwamnati fitar da shi daga gidan.
Saidai David Mark ya garzaya babban kotun tarayya dake Abuja domin dakatar da gwamnatin daga fitar da shi daga gidan da kuma kwace mallakin gidan daga hannun sa.
DUBA WANNAN: Kotu ta yankewa wani maigadi hukuncin zaman gidan yari na wata shida bisa laifin yin barci yayin aiki
Har yanzu kotun bata saurari karar da Mark ya shigar gaban na ta ba.
Gidan shugaban majalisar dattijai dake kan titin Chuba Okadigbo a yankin rukunin gidajen ‘yan majalisu dake Apo a Abuja, yana da girman hekta 1.6 dauke da gidaje guda takwas, a warware da juna, a ciki.
David Mark, Sanatan Najeriya daga jihar Benuwe, ya kasance shugaban majalisar dattijai kafin jam’iyyar sa ta PDP ta fadi zabe a Najeriya ta kuma rasa rinjaye a majalisa.
Kwamitin ya zargi cewar Mark ya mallakawa kan sa gidan ne yayin da yake shugabancin majalisar a kan farashi mai rahusa. An yi kiyasin cewar gidan shugaban majalisar yana da darajar data ketare Naira miliyan 748 a farashi mai rangwame.
Gwamnatin tarayya ta bawa David Mark wa’adin kwanaki 21 ya tattara nasa-ya-nasa ya fice daga gidan shugaban majalisar dattijai
Comments
Post a Comment