An Sake Kaiwa Saudiyya Hari Da Makami Mai Linzami
Gamayyar kasashen da Saudiyya ke jagoranta a yakin da ake yi da ‘yan tawayen Houthi na kasar Yemen ta ce ta tare wani makami mai linzami da aka harba birnin Riyadh, in ji kafafen watsa labaran Saudiyya.
Ganau a babban birnin kasar Saudiyya sun wallafa bidiyo a shafukan sada zumunta da ke nuna hayaki ya turnuke sararin samaniya kuma an ba da rahotannin rushewar wurare.
Gidan talabijin din al-Masirah na ‘yan tawayen Houthi ya bayar da rahoton da ke cewa mayakan kungiyar sun harba makami mai linzami samfurin Burkan-2 kan fadar Yamama.
Ayatollah Khamenei na Iran ‘Hitler’ ne – Yariman Saudiyya
An yi barazanar kai wa Saudiyya hari
Wani makami mai linzami da ‘yan tawayen suka harba a watan jiya ya kusa fada wa kan filin jirgin saman Riyadh.
Saudiyya da Amurka sun zargi Iran da bai wa ‘yan tawayen Houthi makamai masu linzami.
Iran ta musanta zargin.
Tun a shekarar 2015 ‘yan tawayen ke yakar gwamnatin Yemen da kuma gamayyar kasashen da Saudiyya ke jagoranta.
Comments
Post a Comment