MURYAR TALAKA TA BAYAR DA TALLAFIN KAYAN MAKARANTA, LITTAFAI A KARAMAR HUKUMAR MULKIN KAURA NAMODA DA KADDAMAR DA SHUWAGABANNINTA.
A cigaba da yunkurinta na bayar da tata gudunmawa, wajen inganta harkar ilimin jahar Zamfara. Wanda kungiyar ta bullo da shirinta na tallafawa dalibbai da littafan rubutu, Biro, alli da kuma kayan makaranta, tare da tura 'ya'yanta, a cikin makarantun gwamnati domin karantarwa kyauta. Wanda kacokan a wannan shekarar ta maida hankali wajen yi, mai taken Muryar Talaka Educational Support (MES2017).
Kungiyar za ta ziyarci Karamar hukumar KAURA NAMODA domin kaddamar da Shuwagabanninta a wadannan KARAMAR HUKUMAR tare da rarraba kayan karatu da rubutu ga dalibbai da kuma kayan makaranta duk kyauta.
Bikin ya gudana Kamar
WURI: FADAR MAI MARTABA EMIR OF KAURA NAMODA
LOKACI: KARFE 11:00 NA SAFE .
SANARWA: Daga Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau PRO I Muryar Talaka Reshen Jahar Zamfara.
Comments
Post a Comment