Kungiyoyin Ta’Addanci Suna Barazanar Kaiwa Abuja Da Wasu Jihohin Arewa Hari – Inji Amurika Da Birtaniya
Gwamnatocin Birtaniya da Amurka, sun gargadi ‘yan ƙasarsu da ke zaune ko shirin kai ziyara a Abuja, cewa kungiyoyin ta’addanci suna barazanar kai harin bam a babban birnin Najeriya a lokacin bikin Kirisimeti.
Ofishin harkokin kasashen waje da na Commonwealth, FCO da ke Najeriya ta yi wannan gargadin ga ‘yan asalin kasar Birtaniya.
FCO ta ce kimanin ‘yan asalin Birtaniya 117,000 ke ziyarci Najeriya a kowace shekara.
Kofar birnin tarayyar Najeriya
Har ila yau, gwamnatin kasar Amurka ma ta gargadi jama’arta kada su tafi jihohin Adamawa da Bauchi da Borno da Gombe da Jigawa da kuma Yobe har zuwa karshen wannan shekara.
FCO ta rubuta a shafinta ta yanar gizo cewa, ” Haɗari na ta’addanci yafi karuwa a lokacin bukukuwan addini; don haka akwai barazanar ɗaukaka hare-haren ta’addanci a cikin wannan lokacin biki na Kirsimeti da sabuwar shekara”.
” Kungiyoyin ta’addanci sun yi barazanar kai hare-haren bama bamai a wadannan yankunan a wannan lokacin”.
Majiyar mu ta tabbatar da cewar, a makon da ta gabata ne, Ofishin jakadancin kasar Amurka a Najeriya ta ba da irin wannan gargaɗin wanda ta kira ” Sakon al’amuran tsaro ga ‘yan Amurka”.
Comments
Post a Comment