Mutane 4 Sun Mutu Yayinda Makiyaya Suka Kai Hari Wani Gari A Cross River



River
– Mazauna kauyen sun far masu
– An rahoto cewa makiyaya hudu sun mutu

a harin
Rahotanni sun kawo cewa an kashe wasu makiyaya guda hudu bayan an zarge su da yunkurin kai hari garin Mbiabong Ito a karamar hukumar Odukpani dake jihar Cross River.

Jaridar Nation ta rahoto cewa Fulani makiyayan sunyi kokarin shiga garin tare da dabbobinsu amma sai mutanen garin suka far masu a ranar Talata, 5 ga watan Disamba.

Wata majiya a garin tayi ikirarin cewa makiyayan wadanda ke dauke da makamai sun fara harbi amma mazauna kauyen suka ki janyewa sannan suma suka far masu da hari. Wannan yayi sanadiyan da makiyaya hudu suka rasa rayukansu.

Mutane 4 sun mutu yayinda makiyaya suka kai hari wani gari a Cross River
Majiyar tayi ikirarin cewa makiyayan sun dawo da wasu sojoji domin suyi kokarin dawo da dabbobinsu da suka barbazu sanadiyan karawan.

KU KARANTA KUMA: Matasan Niger Delta sun bukaci Atiku da karda ya tsaya takarar shugabancin kasa
An rahoto cewa mazauna kauyen sun tsere bayan sojojin sun fara harbi lokacin da suka shiga garin.

Irene Ugbo wanda ya kasance dan sanda mai hulda da jama’a yace an tura jami’ai yankin domin wanzar da zaman lafiya.

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’