KUNGIYAR MURYAR TALAKA TA BAYAR DA TALLAFIN KAYAN MAKARANTA, GA DALIBBAI DA KADDAMAR DA SHUWAGABANNINTA A KARAMAR HUKUMAR MARU!



A yau Talata 19-12-2017 kungiyar Muryar Talaka ta kasa Reshen Jahar Zamfara. Kai ziyara a Karamar hukumar Maru domin bayar da tallafin kayan karatu ga dalibbai a makarantun Gwamnati da ke wadannan karamar hukumar .

A lokacin ziyarar wadda shugaban kungiyar na Jahar Zamfara, Comrade HAFIZU BALARABE GUSAU. ya jagoranta. Ya bayyana cewa, kungiyar Muryar Talaka ta bullo da wannan shirin ne, domin tallafawa, wajen cigaban bangaren ilimi a wannan jahar. Wanda hakan ne, ya sa kungiyar ta bullo da wannan shirin La'akkari da yadda wasu uwaye su ke da matukar rauni wajen daukar nauyin dawainiyar 'ya'yansu. Haka zalika hakan zai taimaka wajen habbaka sha'anin ILIMI a Jahar Zamfara.

A lokacin da ya ke jawabi shugaban makarantar BANAGA SULE Primary school, Maru. Ya bayyana kungiyar muryar Talaka da cewa "Kungiya ce da ya kamata sauran kungiyoyi su yi koyi da ita.

"Dan Haka ya kamata ku Kara jajircewa wajen aiki tukuru. Musamman ganin cewa kungiyar, ba kungiya ba ce, da ake samun wani muhimmin kaso ba. Illa Dai kasonku na wajen mahaliccinku."

A bangare daya mun kaddamar Shuwagabannin kungiyar muryar talaka reshen karamar hukumar MARU. Wadanda za su zama wakilai gare Mu a wannan karamar hukumar.

Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau PRO I Muryar Talaka Reshen Jahar Zamfara

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’