Hare-Haren Saudiyya Ya Kashe Mutane136 A Kasar Yaman – UN
Majalissar Dinkin Duniya (UN) ta ce hare-haren da kasar Saudiyya da kawayenta su ka kai wa kasar Yaman a cikin kwanaki goma yayi sanadiyar mutuwar fararen hula 136.
Kakakin kungiyar kare hakkin dan Adam dake karkarshin Majalissar Dinkin Duniy, Rupert Colville, ya bayyana haka a lokacin da yake zanatwa da manema labaru a Geneva.
Rupert Colville ya nuna damuwar sa akan sammamen da sojojin Saudiya da kawayenta suke kai wa sojojin yan tawayen kabilar Houthi a Yaman inda suka kashe mutane 136.
Hare-haren Saudiyya ya kashe yan Yaman
Daya daga cikin wuraren da suka kai sumame, har da gidan yarin Sana’a inda mutane 45 suka mutu.
KU KARANTA : Yan tawayen kabilar Houthi sun sake kai wa Saudiyya hari da makami mai linzami
A cikin wannan makon ne yan tawayen kabilar houthi suka harba wa birnin Riyadh dake kasar Saudiya makami mai linzami .
Amma gamayyar kugiyar kasashen da Saudiyya ke jagoranta wajen yakar yan tawayen kabilar Houthi sun ce sun samu nasarar tare makami mai linzami da aka harba kasar Saudiyya.
Comments
Post a Comment