Jami’An Yansanda Sun Yi Caraf Da Wasu Yan Fashi Da Makami Su 23
Rundunar Yansandan Najeriya ta sanar da kama wasu fitinannun yan fashi da makami guda 23 dake tare mutane a kan hanyar Abuja-Kaduna-Suleja har zuwa Minna.
Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ne ya bayyana haka a shafinsa na kafar sadarwar zamani, Facebook, inda yace miyagun mutanen sukan hada da satar mutane, tare da amsan kudaden fansa.
Yansanda sun tabbatar da kama ya fashin da bindigu, alburusai, wukake, kaho, katunan banki da kuma shanun mutane da dama.
Majiyar ta ruwaito rundunar Yansandan jihar Kaduna ta samu nasarar kama wasu samari guda biyu da suka shahara wajen satar mutane a jihar Kaduna, Adamu Lawan, da Aminu Lawan.
Ayyukan masu garkuwa da mutane na cigaba da ta’azzara a jihar Kaduna a yan kwanakin nan, inda miyagun mutanen ke amfani da sabbin salon satar mutane, don a yanzu har almajirai basu bari ba.
Comments
Post a Comment