Posts

Showing posts from October, 2017

Bayan kwashe yan kwanaki baya nan Allah ya masa dawowa.

Image
Bayan kwashe yan kwanaki baya nan Allah ya masa dawowa. Bayan kwashe kwanaki baya nan Allah cikin ikon sa ya masa dawowa kuma yadawo cikin koshin lafiya. Hon,Malam Ridwan bala haske. Muna lale marhabun da zuwan ka. KO shakka babu Kaine farin cikin mutanen Gusau da Tsafe. Kuma ka chanchanci wannan kujerar kuma insha Allahu mu matasa muna Bayan ka. Kasancewar ka mutum Wanda yasan mutuncin Al'umma. Da sanin Yakama ta. Muna maka fatan alkhairi DA fatan Allah yahutar DA gajiya. Daga babban edita na sashen Hausa. A shafukan matasa yan gwaggwarmaya. Comr. Nura Muhammad Mai Apple Gusau

Babachir Da Oke Zasu Fuskanci Tuhuma Daga Hukumomin Yaki Da Rashawa.

Image
Babachir Da Oke Zasu Fuskanci Tuhuma Daga Hukumomin Yaki Da Rashawa. Abinda na fahimta dangane da lamarin Babachir da Oke shine, yanzu bangaren fadar shugaban kasa sun kammala nasu binciken sannan kuma sakamakon binciken ya kawo karshen cin taliyar Babachir da Oke a gwamnatin shugaba Buhari. Yanzu kuma abun zai sauya salo, domin hukumomin yaki da rashawa EFCC ko ICPC su zasu kaddamarda tuhume tuhume akan Babachir da Oke. Wannan ya nuna mana cewar gwamnatin shugaba Buhari tana bin doka da kuma bin matakai daki daki cikin nitsuwa, domin kaucewa cutarda wanda bashi da laifi. A lokuta da dama wasu nayiwa gwamnati mummunar fahimta akan yadda take gudanarda ayyukanta, yayinda suke ganin cewar ana tafiyar hawainiya wajen daukar mataki ko yin hukunci. Abunda mutane basu ankara da shi ba shine, daukar mataki ko yin hukunci cikin gaggawa abune wanda zai iya sa a zalunci wanda yake da gaskiya. Amma idan anbi komi bisa doka da kuma nitsuwa, sai kaga a karshe an sami kyakkyawar sakamako ...

Asiri Ya Tonu!!!

Image
Asiri Ya Tonu!!! Matar Aure Tare Da Kwarton Ta  Sun Mutu A Cikin Mota Turmi Da Tabarya! A Can Jihar Legas Aka Samu Wata Matar Aure Tare Da Kwarto Sun Mutu A Cikin Mota. An Yi Zargin Cewa Ajalinsu Ya Cim Musu Ne A Halin Da Suke Lalata A Cikin Motar. Allah Kara Tona Asirin Maciya Amana Allahumma Amin.

Babu Wata Shawara Da Ta Rage Wa Buhari Illa Ya Fito Takara A 2019 – Ahmed Lawan

Image
Babu Wata Shawara Da Ta Rage Wa Buhari Illa Ya Fito Takara A 2019 – Ahmed Lawan Shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa Ahmed Lawan ya shaida wa manema labarai a fadar shugaban kasa cewa shugaban Kasa Muhammadu Buhari bashi da wata zabi yanzu illa yayi shirin fitowa takara a 2019. Lawan ya fadi haka ne bayan ganawa ta musamman da ya yi da Buhari a gidan gwamnati na Aso Rock. ” Duk abubuwan da Buhari yayi alkawarin yi bayan zama shugaban kasa ya cika su, kamar samar da tsaro da zaman lafiya,  bunkasa tattalin arzikin Kasa, da yaki da cin hanci da rashawa.” Lawan ya ce a dalilin haka duk masoya da magoya bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari na bayan sa kuma suna kira gare shi da ya shirya fitowa takara a 2019. Sanata Abu Ibrahim wanda shine shugaban gamayyar kungiyoyin da suka zama ‘Buhari Support Organisation’ ya ce sun ziyarci shugaban kasa ne don su sanar dashi ayyukan da kungiyar take yi da kuma abin da ta sa a gaba zuwa yanzu.

Babu Kamshin Gaskiya A Dukkanin Zarge-Zargen Da Kungiyar Kiristoci CAN Ke Yiwa Gwamnatin Buhari - Osinbajo

Image
Babu Kamshin Gaskiya A Dukkanin Zarge-Zargen Da Kungiyar Kiristoci CAN Ke Yiwa Gwamnatin Buhari - Osinbajo _______¥_____ Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osibanjo ya caccaki kungiyar Kiristoci ta Nijeriya ( CAN) inda ya yi fatali da zargin da kungiyar ke yi na cewa ana kulla makarkashiyar mayar Nijeriya kasar Musulunci. Mataimakin Shugaban ya nuna takaicinsa kan yadda kungiyar ta mayar da hankali kan duk wasu shirye shirye da suka jibinci Musulunci a maimakon bullo da sabbin ajanda na mabiya Kirista. Tun da farko dai kungiyar CAN ta nuna adawa da kasancewar Nijeriya cikin mambobin Bankin Musulunci sai kuma baya bayan nan da kungiyar ta nuna rashin amincewa da Tsarin Lamuni na SUKUK wanda ke da alaka da Musuluncin wanda aka kaddamar kwanan nan.

SHAFIN MATASA YAN GWAGGWARMAYA SHAFI NE MAI ZAMAN KANSA WANDA KUMA DUNIYAR SOCIAL MEDIA TAKE CI A CIKI!!!

Image
SHAFIN MATASA YAN GWAGGWARMAYA SHAFI NE MAI ZAMAN KANSA  WANDA KUMA DUNIYAR SOCIAL MEDIA TAKE CI A CIKI!!! Assalamu Alaikum. Bayan sallama irin ta Addinin musulunci da fatan kowa yana cikin koshin lafiya,  Alhamdulillahi da samuwar wannan kafa mai Albarka a dai-dai wannan lokaci Mai Albarka. * * * Ko shakka babu wasu jama'a da yawa daga cikin mu sunji dadin bude wannan kafa mai Albarka,  (matasa yan gwaggwarmaya) group facebook da whatsapp  shafuka ne masu zaman kansu wanda kowa zai iya shigarsa kuma ya bayyana Ra'ayinsa dai-dai gwargwado,  amma kuma ra'ayin naka ya kasance Mai ma'ana kuma Wanda bai kaucewa Addinin musulunci ba. * * SHAFIN MATASA YAN GWAGGWARMAYA! Shafi ne na kowa. Kuma a duk inda mutum yake,  cikin jihar Zamfara dama wasu jihohin Najeriya Kwata!   Bayyana ra'ayinka a yau dama kullum. * * Saka sakonni masu muhimmanci a cikin wannan shafin na Matasa yan gwaggwarmaya a facebook group da kuma facebook page da whatsapp. ...

Masu Shayi Sun Koka Da Tsadar Burodi A Kaduna

Image
Masu Shayi Sun Koka Da Tsadar Burodi A Kaduna Wasu masu sayar da shayi a jihar Kaduna, na kokawa game da tsadar burodi, wato abokin tafiyar shayi, duk da faduwar farashin kayayyakin da ake bukata wajen sarrafa shi a kasar. Masu shayin wadanda ke cewa tun da yanzu kayan sarrafa burodi kamar fulawa, da yis da sauransu sun sauka, kamata ya yi masu gidajen burodi su rage farashinsa. Haruna Suleiman wanda aka fi sani da Maikudi mai shayi, shi ne sakatare na kungiyar masu shayi a jihar Kaduna, ya shaida wa wakilinmu cewa, tun da farashin kayan hada burodi sun yi sauki, to ya kamata kungiyar masu yin burodi a ko'ina cikin Najeriya ta yi la'akari da halin da ake ciki a kasar musammam ma dai talakawa, a rage farashin burodi. Maikudi mai shayi, ya zargi masu gidajen burodi da cewa da za a kara samun hauhawar farashin fulawa bayan saukowarta a baya-bayan nan, to da sun kuma tsawwala kudin burodin, duk da yake sun ki saukar da farashinsa a yanzu. To sai dai, shugaban gidan buro...

ANNABI (S.A.W) YA CE AKWAI UKUBA GUDA BIYAR WANDA DUK WANI MUTUM SAI YA HADU DA SU

Image
ANNABI (S.A.W) YA CE AKWAI UKUBA GUDA BIYAR WANDA DUK WANI MUTUM SAI YA HADU DA SU 1. Mutuwa da dacin fitan rai. 2. Kwanciyar kabari da duhunsa. 3. Tambayar kabari da tsananinsa. 4. Hawan siradi da santsinsa. 5. Awon mizani da kididdige shi. SAI SAYYIDINA ABUBAKAR YA CE YA RASULILLAH MENE NE ZAI IYA KARE MU DAGA WADANNAN ABUBUWA GUDA BIYAR? SAI ANNABI (SAW) YA CE: 1. Sallar Asuba cikin jam'i yana hana jin dacin mutuwa. 2. Wanda ya yi sallar Azuhur cikin jam'i za a buda kabarinsa da haske. 3. Wanda ya yi sallar Asri cikin Jam'i za a saukake masa tambayar kabari. 4. Wanda ya yi sallar Magriba ciki Jam'i za a saukake masa hawan Siradi da santsinsa. 5. Wanda ya yi sallar isha'i cikin jam'i za a saukake masa awon Mizani da kididdige shi. WANNAN SHINE KARIYAR DA ANNABI (S.A.W) YA BA MU. . ALLAH YA SA MU DACE DA RAHAMARSA ALBARKAR ANNABI S.A.W. Amin.

Kasar Masar Ta Ba Wa Kanawa Kyautar Gurbin Karatu

Image
Kasar Masar Ta Ba Wa Kanawa Kyautar Gurbin Karatu Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranci mika takardun tallafin karatu ga yan asalin jihar Kano guda takwas 8 a jami'ar Al-Azhar dake garin Alkahira, wanda gwamnatin Masar ta bayar. Gwamna Ganduje ya yabawa gwamnatin Masar bisa wannan tallafi na karatu da ta bayar, wanda shine karo na biyu da suka bayar, domin taimakawa ma su karamin karfi, don su karo ilimi. Hakazalika Gwamna Ganduje ya ce bai yi mamaki ba, ganin irin dumbin tarihin da ke tsakanin Kano da kasar Masar, shekaru da dama. Gwamnan ya ci gaba da cewa yanayin tatabarbarewar tattalin arziki ya sa jihar Kano ta dakatar da tura dalibai karatu kasar waje, inda a har yanzu gwamnati na kokarin sauke nauyin da ta gada ne na daliban da aka tura kasashen waje a gwamnatin baya, saboda haka irin wannan tallafi zai taimaka kwarai wajen ganin an taimakawa masu karamin karfi domin karo ilimi a waje. Daga bisani Gwamnan yayi kira ga daliban da su maida hankali wajen karatun s...

Bauchin Yakubu Na Dab Da Zama Daya Daga Cikin Jihohin Nijeriya Masu Arzikin Mai.

Image
Bauchin Yakubu Na Dab Da Zama Daya Daga Cikin Jihohin Nijeriya Masu Arzikin Mai. Saura kiris Bauchi ta shiga cikin jihohi masu arzikin man fetur a Nijeriya. Buhari da Maikanti Baru aikin ku na kyau, mun gode. Yanzu haka aikin hako man fetur da iskar gas, da gwamnatin talakawa karkashin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ke yi a jihar Bauchi ya yi nisa. An dauki wadannan hotuna ne na a lokacin da gwaman jihar Bauchi Barista Muhammad Abdullahi Abubakar ya kai ziyarar nuna goyon bayan sa akan wannan aiki da gwamnatin Buhari keyi na tono man fetur a jihar Bauchi. Gwamnan Bauchi ya nuna jin dadin sa da wannan aiki wanda yanzu haka ake saka ran cewa daga yanzu  jihar Bauchi za ta shiga cikin jihohi masu arzikin man fetur a Nijeriya. Gwamnan jihar Bauchi ya shaidawa Ma'aikatan da ke gudanar da wanan aiki cewa talakawan jihar Bauchi da ma gwamnatin sa, za su bada hadin kai dari bisa dari domin wannan aiki ya yi nasara. Mu mutanen jihar Bauchi muna fatan alkairi ga gwamnatin talakaw...

Matsalar Rayuwa A Arewa Ga Mace Mai Neman Zama Wani Abu - Rahama Sadau

Image
Matsalar Rayuwa A Arewa Ga Mace Mai Neman Zama Wani Abu - Rahama Sadau A satin da ya wuce, Rahama Sadau ta tattauna da jaridar ThisDay a inda ta yi bayanin halin da take, abunda ta ke so ta cimma, kalubalen da take fama da shi da sauran su. Jarumar ta bayyana rayuwa a arewa a matsayin babban matsalan da take fama dashi domin ta ce arewa ba wuri ba ne da yake encouraging ci gaban mace. Ta kara da cewa har yanxu bata saba koyarwar addini da al'ada ba, amma mutanen Arewa har yanzu suna mata kallon mutuniyar banza bata gari.

Nijeriya Za Ta Iya Amfana Da Tsarin Shugabancin Ƙasar Mexico —Ikweremadu

Nijeriya Za Ta Iya Amfana Da Tsarin Shugabancin Ƙasar Mexico —Ikweremadu Daga Bello Hamza Mataimakin shugaban Majalisar dattawa ta ƙasa, Ike Ekweremadu, ya bayyana cewa, Nijeriya za ta yi natsarin tsarin mulkin ƙasar Mexico na yin shugabanci sau ɗaya ga shugaban ƙasa da gwamnoni, domin fahimtar ko akwai wata moriyar da za ta ci daga irin wannan tsari. Ekweremadu, ya bayyana hakan ne lokacin da Ambasadan Mexico a Nijeriya, Garcia Moreno Elizondo, ya kawo masa ziyara a Abuja, don taya shi murnar cika shekara 57 da samun mulkin kai a Nijeriya. Ya ce, Nijeriya da Meɗico na da abubuwa da yawa da za su amfani junanasu da su, musamman ta fuskar arziƙin wadataccen da kuma tsarin gwamnatin tarayya. A cikin jawabin wanda mai bai wa mataimakin shugaban Majalisar  shawara na musamman  a kan harkokin yaɗa labarai, Uche Anichukwu, Special, ya bayyana cewa, mataimakin shugaban Majalisar ya ce, “Na daɗe da sanin cewa, ƙasar Mexico na da tsarin yin shugaban ƙasa na shekara shida s...

Egypt Ce Ta Biyu Zuwa Kofin Duniya Daga Afirka

Image
Egypt Ce Ta Biyu Zuwa Kofin Duniya Daga Afirka Masar ta zama kasa ta biyu da ta samu tikitin zuwa gasar cin kofin duniya daga Afirka, bayan da ta ci Congo 2-1 a wasan da suka fafata a ranar Lahadi. Mohamed Salah ne ya fara ci wa Masar kwallo bayan da aka dawo daga hutu, saura minti uku a tashi daga karawar Arnold Bouka Moutou ya farke. Daf da alkalin wasa zai tashi karawar Masar ta samu bugun fenariti kuma Mohamed Salah ya buga ya kuma ci kwallon. Da wannan sakamakon Masar ta hada maki 12 a wasa biyar a rukuni na biyar, sai Uganda ta biyu da maki takwas sai Ghana mai maki shida da Congo ta karshe da maki daya kacal. Sauran kasashe uku suka rage da za su cika biyar, domin wakiltar Afirka a gasar cin kofin duniya da Rasha za ta karbi bakunci a 2018. Nigeria ce ta farko daga Afirka da ta fara samun tikitin zuwa gasar cin kofin duniya, bayan da ta jagoranci rukuni na biyu.

El-Rufai Ya Ziyarci Tafa

Image
El-Rufai Ya Ziyarci Tafa Gwamnan jihar Kaduna ya ziyarci garin Tafa, dake karamar hukumar Kagarko, jihar Kaduna. Gwamnan ya tafi garin Tafa ne domin ziyarar gani da Ido na hadarin tankin Mai da akayi a garin. Wata tankin Mai dauke da fetur ta kama da wuta a garin Tafa inda wasu mutane uku suka rasa rayukansu, wasu Kuma suka jikkita. Banyan haka Kuma gidaje da dukiyoyin mazauna garin da yawa sun salwanta a sanadiyyar wutan. Gwamnan El-Rufai ya yi juyayin abin da ya faru sannan Kuma ya Kai ziyarar duba ina aka kwana a aiki da gwamnati ke yi na gina sabon tashan manyan motoci a garin.

Shiga Ta Harkar Fim Na Wucin Gadi Ne, Da Zarar Na Samu Miji Zan Yi Aure - Jarumar Hausa Fim Fati Garba.

Image
Shiga Ta Harkar Fim Na Wucin Gadi Ne, Da Zarar Na Samu Miji Zan Yi Aure - Jarumar Hausa Fim Fati Garba. Fati Garba shahararriyar yan wasan fina-finan Hausa ce da bata dade da shiga harakar ba. Sai dai shigar ta ke da wuya ta ko nuna hazakarta da kwazo wajen nuna cewa ita ma zata iya kara wa da manyan jarumai a farfajiyar fina-finan Hausa. A hira da tayi da manema labarai a Abuja, ta ce Allah ne yayi za ta yi fim a Kannywood domin har ta cire rai. ” Na dade ina neman yadda zan yi in shiga farfajiyar Fina finan Kannywood amma inaa tunda har sai da na hakura ma domin duk ta inda na bi sai kaga ba haka ba. Abin ya gagara.” Fati ta ce dama can tana dan yin wasannnin kwaikwayo a jihar Neja inda tun a wannan lokacin take ta kokarin samun daman shiga Kannywood. ” Cikin Ikon Allah kuwa wata rana wani da na sani ya ce zai sakani a wani fim da yake shiryawa kuma Jarumi Adam Zango ne zai fito a fim din. Nan da nan ko naji kamar ya yi mini Albishir da miliyoyin kudi. Dalili kuwa shine, Ad...

Asibitin Fadar Gwamnati Zai Koma Na Kuɗi

Image
Asibitin Fadar Gwamnati Zai Koma Na Kuɗi Babban Sakataren Fadar Shugaban Ƙasa, Mista Jalal Arabi, a jiya Laraba ya bayyana  cewa hukumar asibtin Fadar Shugaban Ƙasa, za ta nemi damar mayar da asibtin na kuɗi, domin a magance wasu matsaloli da ke addabrsa. Wannan jawabin ya fito ne daga wata sanarwar da mataimakin daraktan yaɗa labarai, na fadar shugaban ƙasa, Mista Attah Esa ya fitar, inda sakataren ya mayar da martani ga wasu rahotanni da ke fitowa kwanakin baya daga kafafen watsa labarai. Arabi ya bayyana cewa mayar da asibitin zuwa na kuɗi zai bayar da wata dama na samar wad a asibitin da hanyar samun kuɗaɗen shiga da kuma rage wa gwamnatin tarayya nauyin kuɗaɗen da take ware mishi, ba kamar yadda a baya a ke tafiya ba, inda ake yi wa kowa aiki kyauta. Ya yi alƙawarin cewa za a sauya wa asibitin fasali, ta yadda komi zai zama ingantacce kuma mai nagarta.

An Kashe Sojojin Amurka A Nijar

Image
An Kashe Sojojin Amurka A Nijar Wasu mahara daga kasar Mali sun yi wa dakarun Nijar da na Amurka kwanton-bauna a garin Tongo Tongo da ke arewacin jahar Tillabery, inda suka kashe sojin Amurka uku da na Nijar biyar, wasu kuma ba a gansu ba a harin da aka kai ranar Laraba. Rahotanni sun ce 'yan bindigar daga Mali sun kai farmaki ne garin da ke kan iyakar Nijar da Mali a ranar Laraba da yamma, amma dakarun Nijar da na Amurka da ke yankin suka koro su. A yayin wannan raraka ne da dakarun na Nijar da Amurkar suka yi musu ne sai 'yan tawayen suka yi musu kwanton-bauna, suka halaka wasu, sannan kuma ba a ga wasunsu ba. Ya zuwa yanzu dai babu wani cikakken bayani game da lamarin da hukumomin Nijar suka fitar. Sojojin Amurka suna bayar da horo da sauran taimako ga takwarorinsu na Nijar domin taimaka musu a yaki da mayaka masu ikirarin jihadi, wadanda suka hada da reshen kungiyar Al Qaeda na Arewacin Afirka. A wani rahoto da Majalisar dinkin duniya ta fitar a baya bayan nan ta ...

Da Musulmi Ne Da Tuni An Kira Shi Dan Ta'adda

Image
Da Musulmi Ne Da Tuni An Kira Shi Dan Ta'adda Rahoton BBC Hausa A yayin da aka samu bayanai game da maharin da ya kashe mutum 59 a birnin Las Vegas na Amurka, muhawara ta barke a kafafen sada zumunta game da abin da ya hana a kira Stephen Paddock da sunan dan ta'adda. An bayyana maharin, mai shekara 64 ne da sunaye kamar: "tsohon akanta" da "kaka" da "dan caca" da "mahari" da "wanda ya kitsa kai harin shi daya", amma babu wanda ya kira shi da sunan dan ta'adda. A kafafen sada zumunta, mutane da dama suna ce idan da a ce Mista Paddock Musulmi ne, to da za a rika kiransa da sunan "dan ta'adda" ne cikin hanzari ba tare da samun wadansu hujjoji da suka alakanta shi da masu tsananin kishin Islama ba. Fitattun mutane da suka hada da malaman jami'a da 'yan wasan kwaikwayo da mawaka suna ci gaba da tambaya game da abin da ya hana a danganta maharin da ta'addanci. Kamar yadda dokar jihar Nevada (w...

Wani Ne Ya Mare Shi Kumatun Ya Koma Haka

Image
Wani Ne Ya Mare Shi Kumatun Ya Koma Haka *Almajiri ne yana karatu a hannun malaminsa a unguwar Wailari karshen Na'ibawa ta kudu a karamar hukumar Kumbotso ta jihar Kano. *Wani ne ya mare shi shi ne kumatunsa ya kumbura sama da wata shida kenan. *Malamin sa ya kai kara wajen 'Yan sanda Amma da yake karfinsa bai kai ba, ba a dauki wani mataki ba. *Bera ya gwaguyi kumburarren kumatun a dalilin haka yanzu ana hango hakoran sa a waje an kuma rasa mai taimaka masa.

Budurwa Ta Hada Baki Da Saurayinta Ya Sace Ta, Don Iyayenta Su Biya Kudin Fansa

Image
Budurwa Ta Hada Baki Da Saurayinta Ya Sace Ta, Don Iyayenta Su Biya Kudin Fansa