Egypt Ce Ta Biyu Zuwa Kofin Duniya Daga Afirka

Egypt Ce Ta Biyu Zuwa Kofin Duniya Daga Afirka

Masar ta zama kasa ta biyu da ta samu tikitin zuwa gasar cin kofin duniya daga Afirka, bayan da ta ci Congo 2-1 a wasan da suka fafata a ranar Lahadi.

Mohamed Salah ne ya fara ci wa Masar kwallo bayan da aka dawo daga hutu, saura minti uku a tashi daga karawar Arnold Bouka Moutou ya farke.

Daf da alkalin wasa zai tashi karawar Masar ta samu bugun fenariti kuma Mohamed Salah ya buga ya kuma ci kwallon.

Da wannan sakamakon Masar ta hada maki 12 a wasa biyar a rukuni na biyar, sai Uganda ta biyu da maki takwas sai Ghana mai maki shida da Congo ta karshe da maki daya kacal.

Sauran kasashe uku suka rage da za su cika biyar, domin wakiltar Afirka a gasar cin kofin duniya da Rasha za ta karbi bakunci a 2018.

Nigeria ce ta farko daga Afirka da ta fara samun tikitin zuwa gasar cin kofin duniya, bayan da ta jagoranci rukuni na biyu.

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’