Babu Kamshin Gaskiya A Dukkanin Zarge-Zargen Da Kungiyar Kiristoci CAN Ke Yiwa Gwamnatin Buhari - Osinbajo

Babu Kamshin Gaskiya A Dukkanin Zarge-Zargen Da Kungiyar Kiristoci CAN Ke Yiwa Gwamnatin Buhari - Osinbajo

_______¥_____

Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osibanjo ya caccaki kungiyar Kiristoci ta Nijeriya ( CAN) inda ya yi fatali da zargin da kungiyar ke yi na cewa ana kulla makarkashiyar mayar Nijeriya kasar Musulunci.

Mataimakin Shugaban ya nuna takaicinsa kan yadda kungiyar ta mayar da hankali kan duk wasu shirye shirye da suka jibinci Musulunci a maimakon bullo da sabbin ajanda na mabiya Kirista.

Tun da farko dai kungiyar CAN ta nuna adawa da kasancewar Nijeriya cikin mambobin Bankin Musulunci sai kuma baya bayan nan da kungiyar ta nuna rashin amincewa da Tsarin Lamuni na SUKUK wanda ke da alaka da Musuluncin wanda aka kaddamar kwanan nan.

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’