El-Rufai Ya Ziyarci Tafa

El-Rufai Ya Ziyarci Tafa

Gwamnan jihar Kaduna ya ziyarci garin Tafa, dake karamar hukumar Kagarko, jihar Kaduna.

Gwamnan ya tafi garin Tafa ne domin ziyarar gani da Ido na hadarin tankin Mai da akayi a garin.

Wata tankin Mai dauke da fetur ta kama da wuta a garin Tafa inda wasu mutane uku suka rasa rayukansu, wasu Kuma suka jikkita.

Banyan haka Kuma gidaje da dukiyoyin mazauna garin da yawa sun salwanta a sanadiyyar wutan.

Gwamnan El-Rufai ya yi juyayin abin da ya faru sannan Kuma ya Kai ziyarar duba ina aka kwana a aiki da gwamnati ke yi na gina sabon tashan manyan motoci a garin.

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’