Skip to main content

Shiga Ta Harkar Fim Na Wucin Gadi Ne, Da Zarar Na Samu Miji Zan Yi Aure - Jarumar Hausa Fim Fati Garba.

Shiga Ta Harkar Fim Na Wucin Gadi Ne, Da Zarar Na Samu Miji Zan Yi Aure - Jarumar Hausa Fim Fati Garba.

Fati Garba shahararriyar yan wasan fina-finan Hausa ce da bata dade da shiga harakar ba. Sai dai shigar ta ke da wuya ta ko nuna hazakarta da kwazo wajen nuna cewa ita ma zata iya kara wa da manyan jarumai a farfajiyar fina-finan Hausa.

A hira da tayi da manema labarai a Abuja, ta ce Allah ne yayi za ta yi fim a Kannywood domin har ta cire rai.

” Na dade ina neman yadda zan yi in shiga farfajiyar Fina finan Kannywood amma inaa tunda har sai da na hakura ma domin duk ta inda na bi sai kaga ba haka ba. Abin ya gagara.”

Fati ta ce dama can tana dan yin wasannnin kwaikwayo a jihar Neja inda tun a wannan lokacin take ta kokarin samun daman shiga Kannywood.

” Cikin Ikon Allah kuwa wata rana wani da na sani ya ce zai sakani a wani fim da yake shiryawa kuma Jarumi Adam Zango ne zai fito a fim din. Nan da nan ko naji kamar ya yi mini Albishir da miliyoyin kudi. Dalili kuwa shine, Adama Zango na daga cikin wadanda nake son in ko da gansu ne mu gaisa a rayuwa ta sai gashi wai zan hadu da shine sannan kuma har kila in yi fim tare da shi.”

” Da yake fim din A Zariya a kayi sai ko gashi na hadu da Adamu Zango. Daga nan ya ce mu hadu a Kaduna inda ya ke shirya wani fin din sa. Aiko muna haduwa sai gashi ya saka ni a ciki kuma ma babban matsayi ya bani. Daga nan kuwa sai likkafata ta ci gaba.”

Fati ta kara da cewa ko yanzu kasuwa ta tashi Dankoli ya ci riba domin da tayi hakuri burinta ya cika. Yanzu tana hidimar Bautar Kasa ce wato NYSC a Kaduna sannan ta ce babu abin da ta sa a gaba yanzu illa shirin Aure.

” Da za ran Allah ya kawo mini miji Zanyi Aure. domin shine yanzu a gabana. Kafinnan kuwa zan ci gaba da yin fim dina har zuwa lokacin.”

Ta jinjina wa jarumai kamar su Ali Nuhu, Aisha Tsamiya, Abdul Shareef, da Umar Shareef, Adam Zango wanda ta ce shine sila na kai wa ga cimma burinta, da sauran ‘yan wasan finan-finan Hausa da take aiki da su.

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Masana sun ce daga cikin abubuwan da suka sa dan Adam yin galaba a kan sauran halittu shi ne yadda yake iya hada kai. Don mutum shi kadai ba zai iya gwada karfi da zaki ko giwa ba. Amma idan ya hada karfi da sauran ‘yan uwansa babu kalubalen da ba za su iya tinkara ba. Hadin kai kuma ba ya tabbata sai da yarda, kuma yarda sai da mu’amala. Masu hikimar magana sun ce, Allah Ya halicce mu da kunne biyu, ido biyu amma sai ya yi mu da baki daya domin mu kalla, mu kuma saurara fiye da yadda muke magana.  Amma sai ya kasance cewa mun fi son yin magana fiye da saurare. Sau da yawa idan muna tattaunawa da wadansu ba ma mayar da hankali kan abin da ake fadi. Kawai jira muke mutum ya kai aya - idan ba mu katse shi ba kenan, domin mu fadi namu ra’ayin. Ga shi kuma ba mu son jin ra’ayoyin da suka sha bamban da namu. To ina za a samu fahimtar juna har a yi aiki tare?  Babu wanda rayuwarsa iri ɗaya da ta wani, kowa da irin  jarabawar shi,  kowa kuma da irin ta shi f...

LABOUR ROOM BLOBAL INITIATIVE KIRA NA MUSAMMAN ZUWA GA MATASA DA 'YAN SIYASA

Duk tarin dukiyarka, ko girman mulkinka ko zamanka basarake, ba zaka taɓa jin daɗin abinda kake taƙama da shi ba, matuƙar al`ummar da kake rayuwa a cikinta ba su zaune lafiya ko da kai ka tsira, kuwa. Shi dama talaka juji ne, duk wani tarin dattin tashin hankali, akansa yake ƙarewa. Da shi ake amfani wajen tashe-tashen hankula, shi ke kisa kuma shi ake kashewa kuma duk masifar da kan biyo baya a kansa ne take sauka. In ko haka ne, haƙiƙa da sake! kenan kowa na matuƙar kaunar zaman lafiya a cikin al'umma, domin sai da zaman lafiya ɗin ne, kowa zai iya morewa, har ya iya rayuwarsa ba tare da shiga tasko ba. A kan haka ne! Ƙungiyar Labour Room Global Initiative haɗin gwiwa da Ƙungiyoyin Jihar Zamfara ke amfani da wannan damar wajan kira ga dukkanin 'yan Siyasa, da ayi siyasa ba tare da gaba ba. Domin in dai har za'a iya zubar da jini a kashe rai a zaɓen fitar da gwani kurrum na jam'iyya ɗaya, to ina ga zaɓen gama-gari da ke tafe? Don haka muna amfani da wannan ...

Ta kashe Mijin ta na aure

Ta kashe Mijin ta na aure Jami'an 'Yan Sanda sun damke wata mata mai shekara 42 ta kashe Mijin ta na aure a wata Unguwa a Garin Legas. Ana zargin Folashade Idoko da kashe Mijin ta a cikin gidan su. Jaridar Daily Post tace wannan mummunan abu ya faru ne a cikin Oto-Awori na Garin Legas. Marigayin dai Injiniya ne kuma tuni dai Jamia'an 'Yan Sanda su kayi ram da wannan mata. Mai gidan hayan da Iyalin su ke yace matar wanda malamar asibiti ce ta dade su na samun matsala da Mijin na ta amma yana hakuri. Kuma dai akwai kishin-kishin din cewa kishin jaraba ne ya sa ta kashe Mijin na ta. Matar dai tace tsautsayi aka samu wuka ta fadi a jikin sa ya mutu. Jami’an tsaro sun damke wani saurayi Ifeanyi Chukwu Maxwell Dike dauke da jikin wata yarinya da aka sace a makon jiya.