Kasar Masar Ta Ba Wa Kanawa Kyautar Gurbin Karatu

Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranci mika takardun tallafin karatu ga yan asalin jihar Kano guda takwas 8 a jami'ar Al-Azhar dake garin Alkahira, wanda gwamnatin Masar ta bayar.
Gwamna Ganduje ya yabawa gwamnatin Masar bisa wannan tallafi na karatu da ta bayar, wanda shine karo na biyu da suka bayar, domin taimakawa ma su karamin karfi, don su karo ilimi. Hakazalika Gwamna Ganduje ya ce bai yi mamaki ba, ganin irin dumbin tarihin da ke tsakanin Kano da kasar Masar, shekaru da dama.
Gwamnan ya ci gaba da cewa yanayin tatabarbarewar tattalin arziki ya sa jihar Kano ta dakatar da tura dalibai karatu kasar waje, inda a har yanzu gwamnati na kokarin sauke nauyin da ta gada ne na daliban da aka tura kasashen waje a gwamnatin baya, saboda haka irin wannan tallafi zai taimaka kwarai wajen ganin an taimakawa masu karamin karfi domin karo ilimi a waje. Daga bisani Gwamnan yayi kira ga daliban da su maida hankali wajen karatun su, kuma Ya baiyana cewa gwamnatin sa zata bawa kowanne dalibi dala dubu daya guzuri.
A nasa jawabin, wakilin kasar Masar kuma shugaban hukumar raya al'adu na kasar masar reshin jihar Kano Dr Ibrahim Ibrahim ya ce wannan tallafi da suka bawa wadannan dalibai su 8, tafi da gidan ka ne hade da kudin makaranta, kudin masauki, kudin abinci, inshora ta lafiya, tikiti na zuwa da komowa, harda kudin kashewa duk wata.
Dr Ibrabim ya kara da cewa, hudu daga cikin daliban zasu shiga makarantar gaba da firamare ne har zuwa jami'a, sannan hudu kuma daga jami'a za su fara. Ya kara da cewa gwamnatin su a shirye suke domin samar wa da wadannan dalibai yanayi mai inganci don ganin sun kammala karatun su cikin nutsuwa.

Comments
Post a Comment