Masu Shayi Sun Koka Da Tsadar Burodi A Kaduna

Masu Shayi Sun Koka Da Tsadar Burodi A Kaduna

Wasu masu sayar da shayi a jihar Kaduna, na kokawa game da tsadar burodi, wato abokin tafiyar shayi, duk da faduwar farashin kayayyakin da ake bukata wajen sarrafa shi a kasar.

Masu shayin wadanda ke cewa tun da yanzu kayan sarrafa burodi kamar fulawa, da yis da sauransu sun sauka, kamata ya yi masu gidajen burodi su rage farashinsa.

Haruna Suleiman wanda aka fi sani da Maikudi mai shayi, shi ne sakatare na kungiyar masu shayi a jihar Kaduna, ya shaida wa wakilinmu cewa, tun da farashin kayan hada burodi sun yi sauki, to ya kamata kungiyar masu yin burodi a ko'ina cikin Najeriya ta yi la'akari da halin da ake ciki a kasar musammam ma dai talakawa, a rage farashin burodi.

Maikudi mai shayi, ya zargi masu gidajen burodi da cewa da za a kara samun hauhawar farashin fulawa bayan saukowarta a baya-bayan nan, to da sun kuma tsawwala kudin burodin, duk da yake sun ki saukar da farashinsa a yanzu.

To sai dai, shugaban gidan burodi na Tahir Bakery a jihar Kaduna, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar masu burodi a Arewacin Najeriya, Alhaji Bashir Tahir, ya ce an samu matsala kwanakin baya a lokacin da gadar Jaba wadda ake bi wajen zuwa Arewacin kasar daga Kudu, ta karye inda hakan ya janyo kayayyakin hadin burodin suka yi karanci a kasuwa.

Alhaji Bashir, ya ce sakamakon karancin kayayyakin, sai farashin kayan hadin burodin ya tashi, to amma an gyara gadar yanzu kaya sun wadata a kasuwa sai dai duk da haka farashin kayan bai koma kamar a baya ba.

Don haka ya ce, yadda ake tunanin kayan sarrafa burodi sun sauka, gaskiya ba su sauka ba.

A kwanan baya dai tsadar burodi ta tilastawa wasu masu cinsa dainawa musamman masu karamin karfi a kasar.

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’