Nijeriya Za Ta Iya Amfana Da Tsarin Shugabancin Ƙasar Mexico —Ikweremadu


Nijeriya Za Ta Iya Amfana Da Tsarin Shugabancin Ƙasar Mexico —Ikweremadu

Daga Bello Hamza

Mataimakin shugaban Majalisar dattawa ta ƙasa, Ike Ekweremadu, ya bayyana cewa, Nijeriya za ta yi natsarin tsarin mulkin ƙasar Mexico na yin shugabanci sau ɗaya ga shugaban ƙasa da gwamnoni, domin fahimtar ko akwai wata moriyar da za ta ci daga irin wannan tsari.

Ekweremadu, ya bayyana hakan ne lokacin da Ambasadan Mexico a Nijeriya, Garcia Moreno Elizondo, ya kawo masa ziyara a Abuja, don taya shi murnar cika shekara 57 da samun mulkin kai a Nijeriya.

Ya ce, Nijeriya da Meɗico na da abubuwa da yawa da za su amfani junanasu da su, musamman ta fuskar arziƙin wadataccen da kuma tsarin gwamnatin tarayya.

A cikin jawabin wanda mai bai wa mataimakin shugaban Majalisar  shawara na musamman  a kan harkokin yaɗa labarai, Uche Anichukwu, Special, ya bayyana cewa, mataimakin shugaban Majalisar ya ce, “Na daɗe da sanin cewa, ƙasar Mexico na da tsarin yin shugaban ƙasa na shekara shida sau ɗaya tak, wanda suke kiransa “seɗino”. Wannan tsari da Nijeriya za ta yi nazari a kansa, saboda akwai matsaloli tattare da tsarin da muke bi a halin yanzu.

“Saboda haka muna duba yiwuwar gyara tsarin mulkinmu wanda zai tabbatar da yin shugaban ƙasa sau ɗaya, don mu rage yawan kashe kuɗin da ake yi wajen gudanar da zaɓuɓɓuka, da gogoriyon neman dawo wa, don a rage almubazzaranci da dukiyar gwamnati”.

“Za mu so mu ji ƙarin haske a gurinka dangane da yadda kuke amfana da tsarin shugabancin ƙasa sau ɗaya, don mu haɗa kai mu ga yadda za mu amfana da irin wannan tsarin”.

Ekweremadu, ya ci gaba da cewa, ya lura jihohi a Mexico na cin gashin kansu  wanda tsarin mulkin ƙasar ya tada musu, saboda haka ƙasar za ta zama mudubi a wajenmu domin amfana da hikimarsu ta gudanar da mulki.

“Saboda haka yanzu za mu ga abin da za mu na ƙarfafa wa jihohi, har ma da ƙananan hukumomi, domin mu rage wa gwamnatin tarayya nauyin da ke kanta. Daga cikin abin da za mu yi na bai wa ƙananan hukumomi cin gashin kansu shi ne, su dinga samun kuɗinsu kaitsaye daga gwamnatin tarayya”.

“Nakan samu kuɗin ƙaramar hukuma ta kaitsaye daga gwamnatin tarayya a matsayina na shugaban ƙaramar hukuma kafin shekara ta 1999. Amma a shekara ta 1999 sai abu ya canza, lokacin da aka kawo wani tsari na asusun haɗaka tsakanin jihohi da ƙananan hukumomi”.

“Sai dai ko a wancan lokacin wasu jihohin sun fake da yin wasu ayyukan da ƙananan hukumomin ke buƙata maimakon su ba su kuɗinsu su yi ayyukansu da kansu. Saboda haka, yanzu za mu yi ƙoƙarin farfafɗo da wancan tsari yadda ƙananan hukumomi za su samu damar tsayawa da ƙafafunsu”

Ekweremadu  ya ci gaba da cewa, Majalisar tarayya za ta ci gaba da ƙoƙarin da take na ganin an samu cin ribar dimokaraɗiyya yadda kowane ɓangare zai samu ‘yancin kansa.

A ƙarshe ambasadan na ƙasar Mexico Elizondo, ya ce, Nijeryia da Mexico na fuskantar ƙalubale iri ɗaya, na ƙoƙarin bunƙasa rayuwar ‘yan ƙasa, saboda haka, in aka zauna aka tattauna za a amfana da juna kamar yadda ya ce.

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’