Da Musulmi Ne Da Tuni An Kira Shi Dan Ta'adda

Rahoton BBC Hausa
A yayin da aka samu bayanai game da maharin da ya kashe mutum 59 a birnin Las Vegas na Amurka, muhawara ta barke a kafafen sada zumunta game da abin da ya hana a kira Stephen Paddock da sunan dan ta'adda.
An bayyana maharin, mai shekara 64 ne da sunaye kamar: "tsohon akanta" da "kaka" da "dan caca" da "mahari" da "wanda ya kitsa kai harin shi daya", amma babu wanda ya kira shi da sunan dan ta'adda.
A kafafen sada zumunta, mutane da dama suna ce idan da a ce Mista Paddock Musulmi ne, to da za a rika kiransa da sunan "dan ta'adda" ne cikin hanzari ba tare da samun wadansu hujjoji da suka alakanta shi da masu tsananin kishin Islama ba.
Fitattun mutane da suka hada da malaman jami'a da 'yan wasan kwaikwayo da mawaka suna ci gaba da tambaya game da abin da ya hana a danganta maharin da ta'addanci.
Kamar yadda dokar jihar Nevada (wato jihar da aka kai harin) ta bayyana ta'addanci: ta ce " ta'addanci shi ne duk wani aiki da ya tada zaune tsaye, wanda ya jawo babbar cutarwa ga jiki, ko asarar rai ga al'umma."

Comments
Post a Comment