Babachir Da Oke Zasu Fuskanci Tuhuma Daga Hukumomin Yaki Da Rashawa.

Abinda na fahimta dangane da lamarin Babachir da Oke shine, yanzu bangaren fadar shugaban kasa sun kammala nasu binciken sannan kuma sakamakon binciken ya kawo karshen cin taliyar Babachir da Oke a gwamnatin shugaba Buhari.
Yanzu kuma abun zai sauya salo, domin hukumomin yaki da rashawa EFCC ko ICPC su zasu kaddamarda tuhume tuhume akan Babachir da Oke.
Wannan ya nuna mana cewar gwamnatin shugaba Buhari tana bin doka da kuma bin matakai daki daki cikin nitsuwa, domin kaucewa cutarda wanda bashi da laifi. A lokuta da dama wasu nayiwa gwamnati mummunar fahimta akan yadda take gudanarda ayyukanta, yayinda suke ganin cewar ana tafiyar hawainiya wajen daukar mataki ko yin hukunci.
Abunda mutane basu ankara da shi ba shine, daukar mataki ko yin hukunci cikin gaggawa abune wanda zai iya sa a zalunci wanda yake da gaskiya. Amma idan anbi komi bisa doka da kuma nitsuwa, sai kaga a karshe an sami kyakkyawar sakamako wacce zata zakulo mai gaskiya ta bashi gaskiyar shi.
Mun amice Baba ka cigaba da bin abubuwa bisa doka da kuma tsaurara bincike kafun hukunci.

Comments
Post a Comment