Asibitin Fadar Gwamnati Zai Koma Na Kuɗi

Babban Sakataren Fadar Shugaban Ƙasa, Mista Jalal Arabi, a jiya Laraba ya bayyana cewa hukumar asibtin Fadar Shugaban Ƙasa, za ta nemi damar mayar da asibtin na kuɗi, domin a magance wasu matsaloli da ke addabrsa.
Wannan jawabin ya fito ne daga wata sanarwar da mataimakin daraktan yaɗa labarai, na fadar shugaban ƙasa, Mista Attah Esa ya fitar, inda sakataren ya mayar da martani ga wasu rahotanni da ke fitowa kwanakin baya daga kafafen watsa labarai.
Arabi ya bayyana cewa mayar da asibitin zuwa na kuɗi zai bayar da wata dama na samar wad a asibitin da hanyar samun kuɗaɗen shiga da kuma rage wa gwamnatin tarayya nauyin kuɗaɗen da take ware mishi, ba kamar yadda a baya a ke tafiya ba, inda ake yi wa kowa aiki kyauta.
Ya yi alƙawarin cewa za a sauya wa asibitin fasali, ta yadda komi zai zama ingantacce kuma mai nagarta.

Comments
Post a Comment