Yawan Haihuwa Ne Silar Talauci A Nijar.
Yawan Haihuwa Ne Silar Talauci A Nijar. Rahoton BBC Hausa Ana tsammanin yawan mutanen Afirka zai rubanya nan da shekarar 2050, amma kasar Nijar wadda aka fi yawan haihuwa a duniya, yawan al'ummarta za su ninka har sau uku. A Nijar, kusan duk mace na haifar 'ya'yan da yawansu ya kai shida zuwa bakwai - ko da yake, yawan haihuwar ya zarce hakan a kauyukan Zinder. Babu mamaki, lamarin ya fi gaban lissafi, domin kusan kowanne kauye ka je - akwai yara ko'ina. Hatta yaran ma suna da yara - fiye da rabin 'yan mata suna aure kafin su kai shekara 15 a duniya. Yayin da tattalin arzikin kasashe ke bunkasa kuma mutane ke daɗa arziki, yawan 'ya'yan da ake haihuwa na raguwa, amma Nijar na cikin jerin kasashen duniya da suka fi talauci. "A Nijar muna da dabi'a ta kasa wadda ke goyon bayan haihuwa, inda ake ganin haihuwar 'ya'ya a matsayin wata alama ta arziki," in ji Dakta Hassane Atamo, shugaban hukumar tsarin iyali ta kasar. "Sa...