Wata Mahajjaciyar Nijeriya Daga Jihar Kogi Ta Rasu A Makkah


Mahajjaciyar jihar Kogi, Hajiya Asma'u Iyawo Abdullahi daga karamar hukumar Igala-Mela ta rasu a Makkah bayan 'yar gajeruwar rashin lafiya.

Shugaban hukumar jin dadin Alhazan jihar ta Kogi, Sheik Lukman Abdullahi Imam shi ya tabbatar da rasuwar a jiya Talata a yayin da yake yin karin haske kan yadda al'amuran mahajjatan jihar ke tafiya a kasa mai tsarki, inda ya ce matar ta rasu ne a safiyar jiya.

Tuni dai aka yi jana'izarta a can kasa mai tsarki. Sannan kuma Sheik Imam ya kara da cewa bacin wannan baiwar Allah da ta rasu, dukkanin mahajjatansu na cikin koshin lafiya.

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’