Yawan Haihuwa Ne Silar Talauci A Nijar.

Yawan Haihuwa Ne Silar Talauci A Nijar.

Rahoton BBC Hausa

Ana tsammanin yawan mutanen Afirka zai rubanya nan da shekarar 2050, amma kasar Nijar wadda aka fi yawan haihuwa a duniya, yawan al'ummarta za su ninka har sau uku.

A Nijar, kusan duk mace na haifar 'ya'yan da yawansu ya kai shida zuwa bakwai - ko da yake, yawan haihuwar ya zarce hakan a kauyukan Zinder.

Babu mamaki, lamarin ya fi gaban lissafi, domin kusan kowanne kauye ka je - akwai yara ko'ina.

Hatta yaran ma suna da yara - fiye da rabin 'yan mata suna aure kafin su kai shekara 15 a duniya.

Yayin da tattalin arzikin kasashe ke bunkasa kuma mutane ke daɗa arziki, yawan 'ya'yan da ake haihuwa na raguwa, amma Nijar na cikin jerin kasashen duniya da suka fi talauci.

"A Nijar muna da dabi'a ta kasa wadda ke goyon bayan haihuwa, inda ake ganin haihuwar 'ya'ya a matsayin wata alama ta arziki," in ji Dakta Hassane Atamo, shugaban hukumar tsarin iyali ta kasar.

"Sakamako na farko na irin wannan yawan haihuwa shi ne ba za a iya ciyarwa da kuma ilmantarwa tare da kulawa da dukkan wadannnan 'ya'yan ba a halin yanzu.

"Daga baya kuma, makomar kasar za ta fuskanci barazana, sai dai idan mun yi amfani da albarkar yawan wadannan yara masu tasowa."

Tattalin arzikin kasar ya dogara ne a kan noma - noman, kusan na iya abin da za a ci a gida ne kawai - kuma idan ba an dauki wani kwakkwaran mataki ba, wata dama ce wadda mai yiwuwa ba za a yi amfani da ita ba.

Saboda haka a kauyen Anguwal Gawo, mutane na samun taimako daga waje kan hanyoyin daidaita tsarin iyali.

A cikin filayen gidajen kasa, wasu 'yan mata na zaune suna tattaunawa ba boye-boye kan shirin hana daukar ciki da auren dole ko kuma matsalolin auren wuri tare da haihuwar wuri.

Wuri ne wanda masu aikin agaji ke kira 'wuri mai aminci' ga 'yan mata - kuma wasunsu ba su wuce 'yan shekara 10 da haihuwa ba.

Saratou Kanana, mai shekara 27, daya ce daga cikin 'yan mata uku da aka ba wa horo domin jagorancin tattaunawar.
Tana da 'ya'ya hudu, amma duk da maganar ba da tazara tsakanin haihuwa da haihuwa, ba za ta iya fadar 'ya'ya nawa take son ta kara haifa ba.

"Ya danganta da abin da Allah ya yi," in ji ta. Amman lamarin ya fi hakan sarkakiya.

Bayan ta kauce wa wata tambayar da aka yi mata ta hanyoyi daban-daban, tafintan sai ya yi bayani daga baya..

A matsayinta na mace ba ta da zabi. Komai ya dogara da mijinta. Idan mijinta ya yanke shawarar daina haihuwa, sannan ne za ta iya zuwa cibiyar kula da lafiya domin dakatar da haihuwa.

"Amma komai ya danganta ne da mijin. Miji shi ne mai iko."

Haka zalika, a daya bangaren garin, maza na zaune karkashin bishiya kuma suna tattaunawa game da irin wadannan abubuwa - suna kiran wurin makarantar angwaye.

Ana cakuda batutuwan kiwon lafiya da ilimi da kuma maganar dawa da tattaunawa game ba da mama da tazarar haihuwa.

Duk da cewar Musa Malam Haru, mai shekara 47, yana jagorancin tattaunawar, yana da mata biyu da 'ya'ya 15, kuma yana tsammanin ya kara akalla biyu ko uku.

Wannan wani bangare ne na shirin - wanda ake kira Shirin Sauki - kuma manufarsa shi ne rage yawan matan da ke mutuwa a lokacin haihuwa da kuma 'ya'yan da ke mutuwa kafin su kai shekara biyar tare da kokarin bunkasa tsarin 'ya'ya kadan.

Idan akwai karin tabbas game da rayuwa, mutane ba sa bukatar 'ya'ya da yawa, matsalar ita ce shawo kan "dabi'ar al'ummar kasar."

Da alama Muɗɗaha Musa, mai shekara 27, ya gamsu cewar yara biyar ko shida sun ishe shi idan ya kara biyu ko uku kan wadanda yake da su yanzu.

Ya amince cewar: "A gaskiya akwai matsala a nan game da haihuwan yara da yawa, amman saboda makarantar angwaye mun fara ganin alfanun hakan."

Da alamar ilimi shi ne hanyar da ta fi dacewa wajen rage yawan 'ya'yan da ake haihuwa.

A wani asibitin tafi-da-gidanka dake da dan nisa daga babbar hanya, wani dan karamin daki yana cike da mata da kananan yara.

Ma'aikatan jinyan na mika takardar hanyoyin hana daukar ciki daban-daban ga mutanen domin su duba.

A wannan wuri, akwai kwaroron roba na maza da na mata da magunguna da kuma abun hana daukar ciki da ake saka wa mata a gaba har ma da tattaunawa game da dasa abun hana daukar ciki a jikin mace.

A wannan lokacin ne, Nana Aisha, mai shekara 28, ta taho gaba ta ce abun da ta yarda da shi ne a dasa mata abun hana daukar ciki a idon kowa duk da tsoron radadin ciwo da kuma hatsari.

"Ina so ne kawai in nuna wa sauran matan, domin akwai jita-jitar da ake yadawa cewa zai iya kasance wani abun da ka iya makalewa cikin tsokar mutum," in ji ta, kuma nan da nan an gama.

Wasu daga cikin matan sun taru a kanta domin su taba hannunta yayin da suke iya ganin abun da aka dasa karkashin fatanta.

Tana da 'ya'ya uku, amman za ta daga sake haihuwa sai nan da shekara uku.

"Mijina mutum ne mai ilimi. Shi da kansa ne yake karfafa min guiwa domin in je cibiyar kiwon lafiya in yi tsarin iyali," in ji ta.

Amma ko kowa ya gamsu, za a dauki lokaci kafin a rage yadda yawan mutane ke karuwa a Nijar.

An yi kiyasin cewar yawan mutanen Nijar zai kai miliyan 68 daga miliyan 21 da ke kasar a yanzu.

"E, al'adar na sauyawa domin matan da kansu ne suka gane cewar haiuwar yara da yawa matsala ce a garesu," in ji ungozoma Furera Umarou.

Ta yi imanin cewar ma'aratan da suka gamsu za su iya haifan 'ya'ya hudu ko biyar maimakon takwas ko tara.

Ana ta maganganu kan "ribar alkallumar al'umma"- karfin matasa ma'aikata na iya zaburar da tattalin arziki daga talauci yayin da yawan haihuwa da kuma mutuwa ke raguwa, amman wannan na bukatar zuba jari da kuma samar da guraben ayyukan yi da matasan za su cika.

"Idan ba mu ci moriyar ribar yawan matasa ba, za mu shiga wani halin ka-kani-ka-yi," in ji dakta Hassane Atamo, shugaban hukumar tsara iyali.

"Wannan zai iya baarzana ga ci gaba da kasancewar kasa kuma zai iya kawo abubuwa kamar ta'addanci da kuma matsalar shige da fice."

A cikin matasa da yawa mara sa aikin yi ka iya shiga cikin jerin bakin haure da ke zuwa Turai ko kuma su fada hannun masu tsatsaurar rayin Islama kamar Boko Haram.

Gagarumin karin yawan mutane matsala ce ta kowa.

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’