Ka fada mana yaushe zaka kashe kanka tunda Buhari ya dawo - MURIC ta tambayi Fayose

Ka fada mana yaushe zaka kashe kanka tunda Buhari ya dawo - MURIC ta tambayi Fayose

Kungiyar nan ta musulmai masu rajin tabbatar da yancin musulmai a Najeriya watau Muslim Rights Concern (MURIC) a turance ta bukaci Gwamnan Ekiti Mista Ayodele Fayose da ya fadawa yan Najeriya wace rana ce ya sanya da zai kashe kansatunda shugaba Buhari ya dawo.

Wannan kiran dai yana kunshe ne a cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar da kuma shugabanta Farfesa Ishaq Akintola ya sanya wa hannu a karshen makon nan da ya gabata.

Shugaban kungiya ya bayyana cewar yana tuni kuma ga Gwamnan Ekiti Ayodele Fayose da ya bayyanawa yan Najeriya ranar da zai cika alkawarinsa na kashe kansa don su zo kallo.

Shugaban ya ci gaba da cewa ya kamata ko wane shugaba ya zama mai rike alkawari don kuwa shinekikar mutum.

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’