Tsokaci Akan Wasu Daga Jawabin Shugaban Kasa

Tsokaci Akan Wasu Daga Jawabin Shugaban Kasa

1. Munanan Kalaman Batanci A Kafafen Sadarwa Na Zamani: A Jawabin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi tsokaci kan yadda 'yan Najeriya suka wuce iyaka wajen jifan juna da munanan kalamai na kiyayya. Bashir Ahmad aiki ya same ka, kana bukatar zama da shugaban kasa domin gwamnati ta kaddamar da wani shirin wayar da kan al'umma bambanci tsakanin 'yancin fadin albarkacin baki da kuma wuce gona.

2. Kasa Daya Al'umma Daya: Shugaban kasa ya koka akan yadda Najeriya ke neman Wargajewa bisa tsarin da aka dora ta na kasa daya al'umma daya. Su wa ye ke neman a ware? Me ya sa? Wanne Kuma mataki aka dauka? Me ye kuma Hukuncin da dokar kasa ta tanadar?

3. 'Yan Siyasa Masu Kunno Wutar Rikicin Addini Ko Kabilanci Domin Manufar Siyasa: Shugaban kasa ya bayyana cewa wadannan gurbatattun mutane za su gane kuren su. Don haka ina amfani da wannan dama domin tunasar da kai cewa, a fara daukar mataki daga KISAN GILLAR FULANI A TARABA. Domin a hawanka mulki shine rikicin kabilanci mafi muni da sojoji suka bayar da tabbacin da an yi mummunan kisan da ko Boko Haram ba su taba yi ba.

Ina yiwa shugaban kasa Barka Da Dawowa Gida Lafiya, tare da Addu'ar Allah Ya ba lafiya da kuma  ikon sauke nauyin da ka dauka. ALLAH Ya taimaki Nijeriya.

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’