SAI DA RUWAN CIKI AKE JANYO NA RIJIYA!!!

Daga Nura Muhammad Gusau


Assalamu Alaikum,
Barka da yau da fatan kuna lafiya. `yan uwana matasa.

Bayan haka ina amfani da wannan damar wajan kara yin kira zuwa ga matasa kuma masu dogon nazari da hangin nesa. Kuma wadan da sunka tsayu wajan fafutukar ganin yan uwansu matasa sunci gaba.

Ko shakka babu wannan zance haka yake. SAI DA RUWAN CIKI AKE JANYO NA RIJIYA inji 'yan karin magana.  Ina munka baro sana'o' in mu wadan da munka gada Uwaye da kakanni, musali mudauki irin noma da kiyo,

Ko shakka babu akwai Albarka mai dinbin yawa ga harkan noma da kiyo. Saboda sune tushen kasa ta NIGERIA,

Amma kash!   Sai dai ba nan gizo yake saka ba. Matasa suna son noma amma kuma babu isashen taki. Wanda su matasa zasu saka domin ibar wadatacen amfanin gona,

Wannan yasa muke kira da babbar murya zuwa ga gwamnatin tarayya da na jihohin mu da su taimakawa manoma da isashen takin zamani domin samun amfanin gona.

Allah yasa mudace!

SAI DA RUWAN CIKI AKE JANYO NA RIJIYA

Daga Nura Muhammad Gusau 08133376020
Dan kishin matasa

Babban Edita na Shafukan DOMIN MATASA YAN GWAGGWARMAYA

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’