Gwamnan Zamfara Yari Ya Tsayar Da Tawagarsa Don Tallafawa Wadanda Hatsarin Mota Ya Rutsa Da Su A Hanya

Daga Yusuf Abubakar, Sokoto
Gwamnan jahar Zamfara, Alhaji Abdulazeez Yari Abubakar wanda ke akan hanya daga Talata Mafara zuwa Sokoto ya tsayar da tawagar ayarinsa don bayar da taimakon gaggawa ga wasu mutane da hatsarin mota ya rutsa dasu akan hanya kusa da 'Dogon Awo' na hanyar Talata Mafara zuwa Sokoto da safiyar yau Talata.
Gwamna Yari wanda ya fito a cikin ruwan sama har ya jike sharkaf yayin da yake bayar da umurnin kwashe wadanda suka ji raunuka, mussaman wani dan karamin yaro dan shekaru 8 a duniya.
Gwamna Yari ya bayar da gudumuwa naira dubu dari biyar anan take tare da umurnin motar daukar marasa lafiya ta gidan gwamnati jahar Zamfara dake tare da ayarinsa da ta kwashe wadanda suka yi raunuka zuwa Babban Asibitin garin Talata Mafara.
Masu bayar da agaji (wanda ya kunshi mai rubutun) sun shafe mintuna fiye da talatin suna jiran zuwan taimakon jami'an hukumar kiyaye haddura ta kasa FRSC, amma babu kamin isowar ayarin na gwamna Abdul-Azeez Yari wanda suka taimaka.
Babu wani jami'a ko daya da yazo duk da wayar da aka buga a ofishin FRSC dake Mafara abin da bai fi kilomita 20 da inda akayi hatsarin ba.
A karshe babu wani taimako sai da Allah Ya kawo gwamnan jahar Zamfara, Abdul'azeez Yari wanda ya tsaya da kansa tare da jami'ansa suka taimaka da motar daukar maras lafiya.
Haka ma ya bayar da gudumuwa na naira dubu dari biyar garesu don taimaka masu sayen magani.
Abin takaici har gwamna da sauran jama'a suka bar wurin da akayi hatsarin babu jami'in hukumar FRSC ko daya wanda yazo duk da yake suna da motar bas da aka tanada don daukar wadanda suka yi hatsari akan wannan hanyar.
Mafi rinjaye jama'a a wurin sun jijjinawa gwamna Yari dangane da kwashe mintuna har fiye da arba'in a cikin ruwan sama yana aikin ceto ga wadanda suka yi hatsari.
Haka ma ya dace jami'an hukumar FRSC na garin Mafara dasu gyara lamarin aikinsu da bayar da agajin gaggawa lokacin da ake bukatarsa don ceto rayuka.
Babu wanda ya rasu a lokacin hatsarin, amma kusan dukkan wadanda ke cikin motar da tayi hatsari sun ki mummunan rauni ga jikinsu.
Yusuf Abubakar
Dan jarida ne

Comments
Post a Comment