Skip to main content

Posts

Yazeed Trust Fund

Operation Taimakon Marayu. Jiya laraba 29/07/2020 gidauniyar Yazeed Trust Fund ta kaddamar da rabon tallafin kayan sallah wa marayu. Wannan aikin alherin da aka saba, ya gudana ne a babban ofishin kungiyar da ke Gusau babban birnin jihar Zamfara.  A lokacin rabon tallafin na kayan sallah, a cikin nasa bawabin shugaban gidauniyar ta Yazeed Trust Fund Comrade Rufa'i Bala UB Gusau ya ce, sun yi wannan nazarin ne  la'akari da muhimmancin haka, kasancewar marayu basu da wani galihu, ya kamata su ma a in ganta rayuwarsu a ranar sallah su fito kamar kowa. Taimakon marayu da marasa galihu a cikin al'umma abu ne da ba sabon ba, domin aikin ne wanda ya kasance kamar jini a cikin jikin (Alh Yazeed Shehu Danfulani mai Doya, Garkuwan Matasan Gusau Lamidon Tsafe) bayar da wannan tallafin ya samu halartar manyan mutane da dama daga cikin har da iyaye mata, da sauran al'umma, wadanda suka shedi wannan aikin alheri. Haka shugaban kwamitin bayar da wannan t...

Sabunta Riyoji a Cikin Gusau!

A yau ne Assabar 18/07/2020 Gidauniyar Yazeed Trust Fund ta gudanar da gyaran wasu riyojin fanfuna a filin na yawo dake shiyar Sabon fege a Cikin gundumar Galadima a karamar Hukumar Gusau ta jihar Zamfara. Gyaran na zuwa ne a daidai lokacin da al'umma ke matukar neman bukatar taimako musamman abunda ya shafi bangaren samar da ruwan sha masu tsafta. A ci gaba da rangadin bayar da kowane irin taimako hadi da bada gudunmuwa a cikin al'umma, tawagar Gidauniyar Yazeed tayi kicibus da wasu riyoji da ake ci gaba da ibar ruwa a ciki, duk da kasancewar akwai kwatoci da sauran wasu ledodi da kayan kazanta. Kai tsaye jakadun Alh Yazeed Shehu Danfulani karkashin jagorancinsa, ta hannun shugaban amintattun gudanarwa na tafiyar, kuma shugaban kungiyar Yazeed Trust Fund Comrade Rufa'i Bala UB Gusau, suka dukufa ka'in da Na'in wajan gyaran riyojin, domin sabuntasu hadi da mayar da su sabbi, ta hanyar saka masu Tayis da kuma yi masu aiki na zamani, domin samar da ruwa masu ts...

Yazeed Trust Fund, Yazeed Network

A ranar Assabar 11/07/2020 wasu daga cikin tawagar jajirtattun kungiyoyin mata 21 sun ka dubi dacewar bayar da lambar yabo ta girmamawa ga Hajiya Aliya Saraki sarakin Yazeed, shugabar kungiyar Yazeed Network. Bayar da wannan kyauta dai na nufin kara mata kwarin gwiwar tashi tsaye wajan kara tanke damarar gwagwarmayar cigaban al'umma. Mai Apple wakili ne, a wasu kafafen watsa labarai daban-daban a kafofin sadarwa daban-daban, ya ziyarci wajan a lokacin bikin karramawar kuma ya kalato mana bayanai daban-daban mabambanta. Kamar yadda zakuji. Kungiyoyin matan 21 wasu da dama daga cikinsu sun samu damar lekawa a wajan bikin. Inda bukin ya samu halartar mutane da dama, wasu daga cikinsu harda jami'an tsaro, da 'yan siyasa, da mawaka. Bikin wanda mafi yawa mata ne, domin su suke da ruwa da tsakki a wajan. Bikin karramawar ya gudana ne a Nafirst Hotel dake shiyar samaru a Gusau babban birnin jihar Zamfara. Wata da muka sakaya sunanta saboda w...

KUNGIYAR YAZEED NETWORK TA KARBI KUNGIYOYIN MATA 7

wasu daga cikin kungiyoyin mata                     ceo founder Yazeed Network Yazeed Network kungiya ce da aka assasa kuma aka bude ta domin tafiya kafada-da-kafada da sauran kungiyoyin dake fafutikar ilmantar da al'umma, hadi da wayar da kan al'umma akan manufofi hadi da bayyana alherai na (Alh Yazeed Shehu Danfulani Mai Doya), wadanda yake yi ga al'umma. Wata jigo daga cikin babbar kungiyar Yazeed Trust Fund ce ta kirkiri kungiyar, domin hada karfi da karfe, wajan wannan gwagwarmaya. Hajiya Aliya Saraki, ita ce shugabar Kungiyar Yazeed Network. A kokarin kungiyar na ganin ta zakulo kungiyoyin mata a sassa daban-daban na jihar Zamfara, a Ranar alhamis din da ta gabata ta karbi wasu gungun kungiyoyin mata 7 wadanda suka jaddada goyon bayansu ga tafiyar (Alh Yazeed Shehu Danfulani Garkuwan Matasan Gusau Lamidon Tsafe). Jawabin shugabar kungiyar a yayin taron ta jinjina wa tawagar wadannan kungiyoyi tare da shan alwas...

SHUGABAR YAZEED NETWORK TA KARBI TAWAGAR MANYAN KUNGIYOYIN MATA DOMIN NUNA GOYON BAYA WAJAN CI GABAN AL'UMMA

Kungiyar Yazeed Network wanda Hajiya Aliya Saraki ke shugabanta, ta karbi tawagar wasu ayarin kungiyoyin Mata domin marawa tafiyar (Alh  Yazeed Shehu Danfulani baya, wannan karbar na zuwa  ne a daidai lokacin da ayyukan alheri ke ci gaba da sauka a cikin al'umma ta hannun Alh Yazeed Shehu Danfulani, Wadannan kungiyoyi sunyi la'akari da muhimmancin dake akwai wajan irin amfanin al'umma, musamman zuwa ga marasa galihu masu kokarin ganin sun dogara da kansu, a lokacin karbar wannan tawagar an gudanar da jawabai da dama mabambanta wasu daga cikinsu shine, shuwagabannin wadannan kungiyoyi sun nuna farin cikinsu  matuka da gaske a kan irin yadda wannan bawan Allah ya himmatu wajan ganin marayu da marasa karfi sun amfana a cikin arzikin da Allah yayi masa. A lokacin jawabin godiya wanda shugabar wannan kungiya ta Yazeed Network Hajiya Aliya saraki tayi matukar nuna farin cikinta a bisa wannan dogon nazari da wadannan bayin Allah su kayi wajan zuwa a hada han...

Shekara Daya; Hon Kabiru Amadu Mai Palace A Sikelin Nazari.

Assalamu alaikum ranka da ya dade barka da warhaka da fatan kana cikin koshin lafiya, ina amfani da wannan dama domin taya ka murnar cika shekara daya a kan jan ragamar jagorancin kananan hukumomin Gusau da Tsafe a majalisar wakilai, mataki na kasa, Allah ya kara  kyakkyawan jagoranci, amin! Ko shakka babu, zamanka a saman wannan kujerar a Gusau da Tsafe wani babban abun nasara ne, kuma abun sam barka ne, idan muka kalli yadda kake gudanar da wannan wakilci a babban birnin tarayyar Kasa. Falsafa da kuma irin tanadi na Demokaradiyya wadda itace adon dan kasa, zamu iya cewa ka taka muhimmiyar rawa wajan ganin ka kashe zaman kashe wando a tsakanin matasa. Wani babban abun sha'awa shi ne; idan muka kalli yadda mutane ke cin gajiyar wakilcinka, zamu iya cewa abun farin ciki ne da jin dadi. Rayuwa; a kowane lokaci babban abun da talaka ke bukata wajan masu rike da madafun iko, shi ne; samar masa da ingantacciyar rayuwa, kama tun daga, lafiya, ilimi, tsaro, ruwan sha, da kum...

Cikar Shekara Daya; Gwamna Matawalle a Sikelin Nazari!

Assalamu alaikum, Ranka ya dade barka da warhaka da fatan ana ci gaba da gudanar da mulkin wannan jiha cikin koshin lafiya. Allah ya sa haka. Ranka ya dade Sir, cike da girmamawa nake ta ya ka murnar cikarka shekara daya a kan karagar jagorancin al'ummar jihar Zamfara, ko shakka babu wannan babban abun farin ciki ne da sambarka. Allah ya maka jagora har zuwan wa'adin mulkinka. Ranka ya dade Sir! A nazarce kwanaki 360 da ka share kana jan ragamar jihar nan, ko shakka babu an samu cigaba a wurare da dama, kuma abun Yabawa ne a bisa wannan. Mu mun san cewa; ko da  Allah madaukakin sarki ya baka jagorancin wannan jihar ka sameta ne a hargitse, cikin wani mummunan yanayi marar dadi, musamman ta fuskar tsaro, wanda a lokacin mutumin jihar Zamfara a kullum cikin fargaba yake sakamakon mummunan ta'adin 'yan ta'adda, wadanda suka yi sanadiyar rasa rayukan dubban mutune, hadi da cilastawa dubban mutane barin muhallansu ba cikin shiri ba. Hakika abun sambarka ne, ...