SHUGABAR YAZEED NETWORK TA KARBI TAWAGAR MANYAN KUNGIYOYIN MATA DOMIN NUNA GOYON BAYA WAJAN CI GABAN AL'UMMA
Kungiyar Yazeed Network wanda Hajiya Aliya Saraki ke shugabanta, ta karbi tawagar wasu ayarin kungiyoyin Mata domin marawa tafiyar (Alh Yazeed Shehu Danfulani baya, wannan karbar na zuwa ne a daidai lokacin da ayyukan alheri ke ci gaba da sauka a cikin al'umma ta hannun Alh Yazeed Shehu Danfulani,
Wadannan kungiyoyi sunyi la'akari da muhimmancin dake akwai wajan irin amfanin al'umma, musamman zuwa ga marasa galihu masu kokarin ganin sun dogara da kansu, a lokacin karbar wannan tawagar an gudanar da jawabai da dama mabambanta wasu daga cikinsu shine, shuwagabannin
wadannan kungiyoyi sun nuna farin cikinsu matuka da gaske a kan irin yadda wannan bawan Allah ya himmatu wajan ganin marayu da marasa karfi sun amfana a cikin arzikin da Allah yayi masa.
A lokacin jawabin godiya wanda shugabar wannan kungiya ta Yazeed Network Hajiya Aliya saraki tayi matukar nuna farin cikinta a bisa wannan dogon nazari da wadannan bayin Allah su kayi wajan zuwa a hada hannu da karfe wajan ci gaba da ayyukan alheri a cikin al'umma, cikin jawabin nata wanda ta fi mayar da hankali kan irin kyakkyawan yanayi da aka samu na zimmar ganin Alh Yazeed Ya yi amfani da abinda yake da shi wajan ganin marasa galihu sun samu fita daga cikin kangin da suke ciki, kuma tayi kira ga masu hannu da shuni a cikin al'umma domin suyi koyi da irin halayyar Alh Yazeed Wajan aikin tawali'u a cikin al'umma.
A cikin jawabin shugabar tayi jinjina ga mata sannan tayi jinjina ga dukkan magoya bayan Alh Yazeed Shehu Danfulani, haka tayi kira ga matan da suka dubi yiyuwar bin wannan tafiya da su jajirce domin ko ba komai an san mata da jajircewa ga abinda ya shafi harkar sa kai, a karshe tayi addu'ar samun dukkan nasara tare da fatan watsewa lafiya.
A dayan bangare limamin kawo sauyi mai ma'ana a cikin al'umma, kuma shugaban gwagwarmayar Alh Yazeed Shehu Danfulani, wato Comrade Rufa'i Bala UB Gusau, yayi dan takaitaccen jawabi, sannan ya nemi hadin kai da goyon baya domin nasarar tafiyar.
Idan dai zamu ita tunawa ko in ce idan muna biye sau da kafa zamu kasance cikin wasu daga cikin wadanda suka shedi ayyukan alherin wannan bawan Allah na zahiri, kama tun daga daukar nauyin yara zuwa makarantu hadi da daukar nauyin dawayniyarsu, domin ganin suma sun kasance abun moriya a cikin al'umma. Haka mun shedi irin yadda yake taimakon al'umma ta bangaren samar da ruwan sha, hadi da gyaran masallatai da bayar da tallafi a asibitoci da sauran ayyukan da lokaci ba ba zai bamu damar zaiyanuwa ba.
a nan muna amfani da wannan damar domin addu'ar samun dukkanin nasara ga tafiyar Alh Yazeed Shehu Danfulani, kasancewarsa mutum mai son ci gaban al'umma.
Rahoto, Daga Nura Mai Apple, Media Reporter Zamfara Najeriya.
Comments
Post a Comment