Sabunta Riyoji a Cikin Gusau!
A yau ne Assabar 18/07/2020 Gidauniyar Yazeed Trust Fund ta gudanar da gyaran wasu riyojin fanfuna a filin na yawo dake shiyar Sabon fege a Cikin gundumar Galadima a karamar Hukumar Gusau ta jihar Zamfara. Gyaran na zuwa ne a daidai lokacin da al'umma ke matukar neman bukatar taimako musamman abunda ya shafi bangaren samar da ruwan sha masu tsafta.
A ci gaba da rangadin bayar da kowane irin taimako hadi da bada gudunmuwa a cikin al'umma, tawagar Gidauniyar Yazeed tayi kicibus da wasu riyoji da ake ci gaba da ibar ruwa a ciki, duk da kasancewar akwai kwatoci da sauran wasu ledodi da kayan kazanta.
Kai tsaye jakadun Alh Yazeed Shehu Danfulani karkashin jagorancinsa, ta hannun shugaban amintattun gudanarwa na tafiyar, kuma shugaban kungiyar Yazeed Trust Fund Comrade Rufa'i Bala UB Gusau, suka dukufa ka'in da Na'in wajan gyaran riyojin, domin sabuntasu hadi da mayar da su sabbi, ta hanyar saka masu Tayis da kuma yi masu aiki na zamani, domin samar da ruwa masu tsafta a cikin al'umma.
Babban wani abun sha'awa shine irin yadda al'ummar wannan yanki sun ka nuna farin cikinsu marar misaltuwa a lokacin gudanar da aikin, gungun matasa hadi da dattawa, da matan wannan yanki sun nuna matukar farin cikinsu, hadi da sambarka. Tare da addu'a da fatan alheri.
Wani abun sha'awa shine, wani fitaccen malamin addinin islama dake a yankin mai suna; Malam Dan Hajo, wanda kuma shine wanda yayi addu'ar bude wadannan rojiyoyi yace ko shakka babu, shi yafi kowa sanin halin Alh Yazeed Domin kuwa a makarantarsa yayi karatu shi da ahalinsa, sannan ya samu kyakkyawar tarbiyya shiyasa ba yayin kasa a gwiwa wajan gudanar da ayyukan alheri a cikin al'umma. Sannan ya kara da jan hankali akan fadada wannan hidima a nan gaba, wajan yin irin wadannan gyare-gyare a makarantun allo wadanda ke matukar bukatar hakan.
A lokacin da muka tuntubi daya daga cikin jiga-jigan tafiyar Alh Yazeed Shehu Danfulani, kuma jigo a Gidauniyar Yazeed Trust Fund, Kaura Na Madina, ya tabbar da cewar wannan ba shine karo na farko ba, na gudanar da aikin sabunta riyoji a cikin Gusau babban birnin jihar Zamfara.
A lokacin da muka mayar da abin magana ga shugaban tafiyar, wato COMRADE UB GUSAU, ya ce ya kara da jaddada mana cewar ko shakka babu ire-iren wadannan ayyukan ba zasu kyargu ba, sannan za'a cigaba da gudanar da su a cikin al'umma, ba tare da nuna bambanci ba.
Idan dai masu karatu zasu iya tunawa, ko in ba su manta ba, mun sha kawo maku wasu kadan daga cikin ayyukan alherin da Alh Yazeed Shehu Danfulani yake a cikin al'umma. Domin ganin ya bayar da duk wata gudunmuwar da ake bukata iya karfinsa.
Kama tun daga makarantu, daukar nauyin karatu, samar da ruwan sha. Kiyon lafiya. Da sauransu.
A karshe muna addu'ar Allah ya ci gaba da taimakon Alh Yazeed Shehu Danfulani, Garkuwan Matasan Gusau Lamidon Tsafe, a kan manufofinsu na alheri a cikin al'umma.
Fatan Alheri Gusau
Fatan Alheri Zamfara
Fatan Alheri Najeriya
fatan Alheri Afrika
Comments
Post a Comment