Shekara Daya; Hon Kabiru Amadu Mai Palace A Sikelin Nazari.




Assalamu alaikum

ranka da ya dade barka da warhaka da fatan kana cikin koshin lafiya, ina amfani da wannan dama domin taya ka murnar cika shekara daya a kan jan ragamar jagorancin kananan hukumomin Gusau da Tsafe a majalisar wakilai, mataki na kasa, Allah ya kara  kyakkyawan jagoranci, amin!

Ko shakka babu, zamanka a saman wannan kujerar a Gusau da Tsafe wani babban abun nasara ne, kuma abun sam barka ne, idan muka kalli yadda kake gudanar da wannan wakilci a babban birnin tarayyar Kasa.

Falsafa da kuma irin tanadi na Demokaradiyya wadda itace adon dan kasa, zamu iya cewa ka taka muhimmiyar rawa wajan ganin ka kashe zaman kashe wando a tsakanin matasa. Wani babban abun sha'awa shi ne; idan muka kalli yadda mutane ke cin gajiyar wakilcinka, zamu iya cewa abun farin ciki ne da jin dadi.


Rayuwa; a kowane lokaci babban abun da talaka ke bukata wajan masu rike da madafun iko, shi ne; samar masa da ingantacciyar rayuwa, kama tun daga, lafiya, ilimi, tsaro, ruwan sha, da kuma tallafa masa ta fuskar cigaban kasuwanci, noma da kiyo, da sauransu.

Ranka ya dade! Tun bayan kammala gwagwarmayar neman samun 'yanci, wadda ko shakka babu, mun tabbatar da cewar yunkurin jama'a da kuma nuna so da kaunarsu, da kuma dukufa ka'in-da-na'in wajan addu'o'i da taimakon Allah ne silar samun dukkan nasarar da a ka samu a cikin lokacin da aka fito da wanda ake kai a yanzu da inda za a dosa a nan gaba.

Ranka ya dade kasancewarmu tare da kai, da kuma bibiye da kai, a sha'anin yau da kullum. Ko shakka babu mun fi kowa farin ciki idon har muka ga ka samu nasarar kaso 80/100 a sha'anin jagorancinka a wajan al'ummarka.

Ko shakka babu, idan aka aunaka da sauran takwarorinka wadanda suka rike madafun iko a yanzu, da kuma wadanda suka rike irin wannan matsayi kaminka, zamu iya cewa ka ciri tuta. Domin ko ba komai matasa dama sun amfana ta fuskoki dama mabambanta.

Shekara daya, ma'aunin adalci baya isa a dubi gazawarka, kasancewar idan dambu ya yawa baya jin mai. To amma ranka ya dade muna kara kyautata maka zato inda mu kaga zawarka. Kasancewar dan Adam ajizi!


Bisa girmamawa, ranka ya dade, mun shedar a 'yan kwanakin baya ka shirya wani zaman jin koken al'umma, wanda ya gudana a karamar hukumar Tsafe, inda aka shirya zaman domin ji, hadi da karbar koken talakawa, da kuma shawarwarin al'umma akan irin yadda ake tafiyar da sha'anin wakilci, ko shakka babu a zahiri mun yaba matuka ainun a bisa wannan.

Jinjina ta musamman; muna jinjina maka akan irin yadda kayi tsayuwar daka domin jindadi hadi walwalar al'ummarka, a cikin shekara daya tal...!


Shawara;

Tsaro; matsalar tsaro babbar matsala ce wadda kafatanin duniya babu wata kasa da bata fuskantar tarnaki a sha'anin tsaro. Kasancewar tsaro shine  babban jigo kuma sai da shine sannan al'umma zata samu dukkan cigaba, ko shakka babu yanzu kananan hukumomin Gusau Da Tsafe sun samu sassaucin matsalar tsaro sosai, idan muka kwatanta da lokacin baya, to amma ranka ya dade a kara matsa kaini, ta wannan fuskar.

 Domin ganin an kara samar da matakan da suka kamata, don ganin zaman lafiya ya cigaba da dorewa a wadannan kananan hukumomi da muke da su, a Gusau da Tsafe, da sauran yankuna da sassan jihar nan baki daya.

Fatara; ranka ya dade, akwai kauyuka da dama, a karkashin wadannan kananan hukumomi suna matukar bukatar agajin gaggawa/gaugawa, saboda suna cikin halin matsi da kuncin rayuwa, musamman yankunan kwaran Ganuwa, yankin Keta, da kuma yankin Wara-wara, da sauransu.

Fannin lafiya; kasancewar shi aikin alhiri bashi da kadan; ranka ya dade akwai bukatar ka samar da 'yan dakunan shan magani a wadannan yankuna, domin su san da cewa ba'amanta da su ba, musamman masu ganin kamar sun tura mota ce tana kokarin madesu da kura. Hakan zai matukar tasiri da kuma tuna alherinka tare da yi maka addu'a a lokacin da ran wani ya farantu ta sanadiyar haka.

Ruwan sha; kasancewar rayuwa sai da ruwa, akwai bukatar mutanen karkara, su samu 'yan kananan riyoji ko murtsatse, domin samun isassun ruwa sha,  hakan zai matukar taimaka wajan inganta rayuwarsu.

Fanni Ilimi; duk da munsan kayi kokari matuka ainun ta wannan fanni, to amma muna cike da fatan ganin wannan shekarar kokarinka zai lunka, wajan samar da ilimi a tsakanin matasa, domin hakan zai taimaka ga matasa su dogara da kansu, kuma zai sa matasan suyi alfahari da kai, kowane matsayi suka kai a rayuwa.


Fannin Noma; kasancewar al'ummarka kaso mai tsoka manoma ne, (Hon) , akwai bukatar manoman wadannan yankuna su sharbi wannan romo, ta hanyar basu tallafi kayan aikin gona, don wadata wannan aiki da abinci.

Akwai babe da dama da lokaci ba zai bamu damar fada ba, to amma muna fatan zaka baiwa marar da kunya, don kafa tarihin da ba'a taba kafawa ba a Gusau da Tsafe. A karshe ba zamu yi kasa a gwiwa ba, wajan bayar da shawarwari matukar ana bukatar hakan, kuma in bukatar hakan ta tusgo.

Ina maka addu'ar Allah ya zama gatanka, kuma ya maka kyakkyawan jagoranci, ina rokon Allah kar ya barka da dabararka Allah ya shige maka gaba.

Allah ya yi Albarka ga Gusau da Tsafe.

Allah ya yi Albarka ga Zamfara ta Tsakkiya.

Allah ya yi albarka, ga jihar Zamfara.

Allah ya yi albarka ga Arewa

Allah ya yi albarka ga Najeriya da Afrika da Duniyar Musulmai kwata!

Daga Naka Mai son cigabanka ta kowane fanni na rayuwa, kuma abokin gwagwarmayarka. Nura Mai Apple 08133376020

Comments

  1. Shawara itace a dinga ankara Don akwai matsaloli da Yake fuskanta domin akwai wasu Yan kura kurai wadanda baka rasa ba na zaman Dan Adam ajizi Amma hon yayi iya kokarinsa sai dai akwai masoyansa wadanda suka wahala dashi dayawa Amma ya watsa su ya dau wadanda suke adawa dashi yayi kokari ya gyarota da mutanenshi domin Babu wata barazana da Yake samu yanzu face ta al'umma wadanda dayawansu masoyanshi ne.

    ✍️Ahmad Ibrahim ck

    ReplyDelete

Post a Comment

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’