Yazeed Trust Fund
Operation Taimakon Marayu.
Jiya laraba 29/07/2020 gidauniyar Yazeed Trust Fund ta kaddamar da rabon tallafin kayan sallah wa marayu. Wannan aikin alherin da aka saba, ya gudana ne a babban ofishin kungiyar da ke Gusau babban birnin jihar Zamfara.
A lokacin rabon tallafin na kayan sallah, a cikin nasa bawabin shugaban gidauniyar ta Yazeed Trust Fund Comrade Rufa'i Bala UB Gusau ya ce, sun yi wannan nazarin ne la'akari da muhimmancin haka, kasancewar marayu basu da wani galihu, ya kamata su ma a in ganta rayuwarsu a ranar sallah su fito kamar kowa.
Taimakon marayu da marasa galihu a cikin al'umma abu ne da ba sabon ba, domin aikin ne wanda ya kasance kamar jini a cikin jikin (Alh Yazeed Shehu Danfulani mai Doya, Garkuwan Matasan Gusau Lamidon Tsafe)
bayar da wannan tallafin ya samu halartar manyan mutane da dama daga cikin har da iyaye mata, da sauran al'umma, wadanda suka shedi wannan aikin alheri.
Haka shugaban kwamitin bayar da wannan tallafi wanda ke a karshin jagorancin shugaban tafiyar Comrade UB ya yi kira da babbar murya ga daukacin al'ummar musulmi musamman masu hannu da shuni domin suyi koyi da mai gidan nasa, wajan bayar da taimako ga marasa galihu, da marayu domin ganin sun yi sallah cikin walwala da annushuwa.
Jawabai da dama da suka gabata a wajan, sun fi mayar da hankali ne kacokan wajan yin kira ga manyan mutane domin taimakon al'umma ta kowane hauji, musamman talakawa masu rayuwar hannu baka hannu kwarya !
Marayun da tallafin ya je hannunsu babu wani shamaki, dukkansu farin ciki a fuskarsu baya misaltuwa, saboda sun samu kayan sallar da zasu fito kamar kowa, sannan sun yi addu'ar Allah ya saka wa da (Alh Yazeed Shehu Danfulani) da mafificin alheri, yayi masa jagora hadi da bashi kariya ga dukkan wani abun ki.
Duk wanda ya faranta ran maraya, shima Allah zai faranta nasa, wannan hadisi ne!
Copyright©nuramaiapple2020

Comments
Post a Comment