Yazeed Trust Fund, Yazeed Network
A ranar Assabar 11/07/2020 wasu daga cikin tawagar jajirtattun kungiyoyin mata 21 sun ka dubi dacewar bayar da lambar yabo ta girmamawa ga Hajiya Aliya Saraki sarakin Yazeed, shugabar kungiyar Yazeed Network. Bayar da wannan kyauta dai na nufin kara mata kwarin gwiwar tashi tsaye wajan kara tanke damarar gwagwarmayar cigaban al'umma.
Mai Apple wakili ne, a wasu kafafen watsa labarai daban-daban a kafofin sadarwa daban-daban, ya ziyarci wajan a lokacin bikin karramawar kuma ya kalato mana bayanai daban-daban mabambanta. Kamar yadda zakuji.
Kungiyoyin matan 21 wasu da dama daga cikinsu sun samu damar lekawa a wajan bikin. Inda bukin ya samu halartar mutane da dama, wasu daga cikinsu harda jami'an tsaro, da 'yan siyasa, da mawaka. Bikin wanda mafi yawa mata ne, domin su suke da ruwa da tsakki a wajan.
Bikin karramawar ya gudana ne a Nafirst Hotel dake shiyar samaru a Gusau babban birnin jihar Zamfara.
Wata da muka sakaya sunanta saboda wasu dalilai, a cikin jawabinta ta ce; sun dubi yiwuwar karrama Hajiya Aliya ne saboda kokarinta a cikin tafiyar Alh Yazeed Shehu Danfulani Mai Doya.
Shugabar Mata ta Gidauniyar Yazeed Trust Fund hajiya Maryam Danfuloti, a cikin jawaban nata tayi matukar nuna farin cikinta, a bisa wannan abun alheri, inda tace tana alfahari da duk wani abun ci gaba da za'a samar a karkashin jagorancinta, saboda haka wannan babban abun yabawa ne.
Daya bangaran Shugaban amintattu na tafiyar Alh Yazeed Shehu Danfulani, kuma shugaban Gidauniyar Yazeed Trust Fund Comrade Rufa'i Bala U&B salanken Galadima, shima ya tofa albarkacin bakinsa, sannan ya yi nuni da cewa kowane lokaci tafiyar Yazeed cike take da gagarumar nasara, inda a karshe yayi addu'ar Allah ya sa kowa ya koma gida lafiya.
A wajan taron wakilinmu ya shedar da ganin wasu daga cikin fuskokin 'yan fafutikar tafiyar gidan Alh Yazeed Shehu Danfulani. Wadanda suka hada da;
Hajiya Maryam Danfuloti
Hajiya Aisha 'yar Asali
Hajiya Mai Glass
Comrade UB Shugaba
Abdurrahaman
zayyanu Dan Mamman
Maikaji Sarkin Yakin Yazeed
Basheer Isiya Figo
Kaura Namadina kauran Yazeed
da sauran mutane da dama.
A lokacin jawabin nata Sarakin ta nuna matukar farin cikinta, a bisa wannan karamci da aka nuna mata, da kuma dubin cancantarta hadi da dogon nazarin bata wannan lambar yabo ta girmamawa. Sannan tayi addu'a ga 'yan uwa da abokan arziki hadi da masu yi mata fatan alheri da sun ka samu damar karba wannan goron gayyatar. Hadi da addu'ar Allah ya kara dafawa Alh Yazeed Shehu Danfulani, domin kara ci gaba da taimakon marasa galihu.
Mai Apple Media Reporter
Comments
Post a Comment