KUNGIYAR YAZEED NETWORK TA KARBI KUNGIYOYIN MATA 7

wasu daga cikin kungiyoyin mata

                    ceo founder Yazeed Network

Yazeed Network kungiya ce da aka assasa kuma aka bude ta domin tafiya kafada-da-kafada da sauran kungiyoyin dake fafutikar ilmantar da al'umma, hadi da wayar da kan al'umma akan manufofi hadi da bayyana alherai na (Alh Yazeed Shehu Danfulani Mai Doya), wadanda yake yi ga al'umma.

Wata jigo daga cikin babbar kungiyar Yazeed Trust Fund ce ta kirkiri kungiyar, domin hada karfi da karfe, wajan wannan gwagwarmaya. Hajiya Aliya Saraki, ita ce shugabar Kungiyar Yazeed Network.

A kokarin kungiyar na ganin ta zakulo kungiyoyin mata a sassa daban-daban na jihar Zamfara, a Ranar alhamis din da ta gabata ta karbi wasu gungun kungiyoyin mata 7 wadanda suka jaddada goyon bayansu ga tafiyar (Alh Yazeed Shehu Danfulani Garkuwan Matasan Gusau Lamidon Tsafe).

Jawabin shugabar kungiyar a yayin taron ta jinjina wa tawagar wadannan kungiyoyi tare da shan alwashin hada karbi tare da su domin aiki tukuru wajan samun kowace irin nasara da ake bukata.

Sarakin, ta jinjina wa (Alh Yazeed Shehu Danfulani a bisa kyawawan manufofinsa a kan al'ummarsa tare da bayar da tabbacin wadannan manufofi za su ci gaba da gudana cikin iyawar Allah. A karshe tayi addu'ar Allah ya sakawa wadannan kungiyoyi da mafificin alheri.

Jawaban da suka gabatar shuwagabannin wadannan kungiyoyi sun nuna farin cikinsu akan irin yadda aka tarbesu hannuwa biyu, duba da ganin suma akwai rawar da suke iya takawa wajan ci gaba da yaɗa manufofin Yazeed.

Daya gefen Shugaban gudanarwa na Tafiyar Yazeed Trust Fund. (Comrade Rufa'i Bala UB Gusau),
a nasa jawabin ya taba muhimman batutuwa, daga ciki yana cewar, duk da kasancewar (Alh Yazeed Shehu Danfulani) baya rike da wata kujerar siyasa a Jihar Zamfara, to amma irin ayyukan da yakeyi don Al'umma abun koyi ne. Ya ce; wani babban abun farin ciki shine yadda  '' Yara Masu Daraja'' ne gaban (Alh Yazeed Shehu Danfulani).

taron ya gudana, kuma ya kammala cikin ƙoshin lafiya. A cikin taron akwai abokanin  aiki waɗanda suka tsakaya domin jajircewar samun cikakkiyar nasara.



Rahoto; Daga Nura Mai Apple. Media Reporter 08133376020


Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’