Skip to main content

Cikar Shekara Daya; Gwamna Matawalle a Sikelin Nazari!




Assalamu alaikum,

Ranka ya dade barka da warhaka da fatan ana ci gaba da gudanar da mulkin wannan jiha cikin koshin lafiya. Allah ya sa haka.

Ranka ya dade Sir, cike da girmamawa nake ta ya ka murnar cikarka shekara daya a kan karagar jagorancin al'ummar jihar Zamfara, ko shakka babu wannan babban abun farin ciki ne da sambarka. Allah ya maka jagora har zuwan wa'adin mulkinka.

Ranka ya dade Sir! A nazarce kwanaki 360 da ka share kana jan ragamar jihar nan, ko shakka babu an samu cigaba a wurare da dama, kuma abun Yabawa ne a bisa wannan. Mu mun san cewa; ko da  Allah madaukakin sarki ya baka jagorancin wannan jihar ka sameta ne a hargitse, cikin wani mummunan yanayi marar dadi, musamman ta fuskar tsaro, wanda a lokacin mutumin jihar Zamfara a kullum cikin fargaba yake sakamakon mummunan ta'adin 'yan ta'adda, wadanda suka yi sanadiyar rasa rayukan dubban mutune, hadi da cilastawa dubban mutane barin muhallansu ba cikin shiri ba.

Hakika abun sambarka ne, tare da farin ciki, idan mukayi la'akari da yadda ka himmatu wajan ganin al'umma sun samu kwanciyar hankali. Ranka ya dade, ɓullo da hanyoyin yin sulhu da waɗannan bayin Allah, ya taka muhimmiyar rawa matuƙa gaya, wajan rage tashe-tashen hankula, wannan mataki abun aya ba ne.

Ranka ya dade, a gyafe daya haka al'ummar jihar Zamfara sun yaba matuƙa a lokacin da ka mayar da mutanen da sun ka rasa ayyukansu a tsohowar gwamnatin da ta gabata, domin hakan ya faranta rayyukan waɗanda lamarin ya shafa wanda kuma mafi yawansu talakawa ne masu dan karamin karfi.

Kuma ranka ya dade Sir! A cikin wannan shekarar da ta gabata mun shedi kokarinka wajan daukar 'ya'yan talakawa har mutum 250 zuwa kasashen ketare daban-daban domin karantar fannin lafiya, don su dawo domin taimakama 'yan uwansu, shima wannan abun farin ciki ne.

A wata kuma mai kama da wannan, duk a cikin shekarar daya, mun shedi yadda ka cika gwamnatinka da matasa, kasancewar sune  kashin bayan cigaban kowace al'umma a duniya, sannan sune masu tasowa. Kuma sune masu bukatar gina rayuwa domin a samu ingantacciyar al'umma.


Abun a jinjina maka ne, irin yadda muka ga kayi namijin kokari a lokacin samun bullor cutar nan mai sarke numfashi ta Korona, kusan zamu iya cewa kana daya daga cikin sahun jerin gwanon gwamnonin da sun ka nuna kulawarsu matuka ainun wajan tashi tsaye domin yaki da wannan cuta har Allah ya kaddara ka samu cikakkiyar nasarar kakkaɓe cutar a cikin jiharka , domin kishin al'ummarka, wannan sashe ka cancanta ayi kwaikwayo da kai, sannan gwamnoni su nemi karin haske daga wajanka akan hanyoyi da kuma dabarun da kayi amfani da su wajan kone wannan cuta a cikin jiharka.

Walwala da jin dadin al'umma, nan ma zamu iya cewa kayi iya kokarinka, wajan sassauta dukkan wata doka da aka sanya domin kandagarkin yaduwar cutar korona. Ko shakka babu a dukkanin waɗannan abubuwa al'ummar jihar Zamfara suna godiya sosai.


Ranka ya dade mai girma gwamna ( Rt Hon Bello Muhammad Matawallen Maradun) muna fatan wannan shekarar zaka zage damtse ta wannan fanni, domin yana matukar bukatar kulawarka.

Ranka ya dade, har yanzu kananan asibitocin karkara da ake kira Primary Health Care suna matukar bukatar kulawarka, domin har yanzu mutanen karkara suna dandana kudarsu kafin su samu masu duba lafiyarsu a lokacin da suka ziyarci ire-iren waɗannan asibitoci. Muna fatan ranka ya dade zaka inganta wannan tsari, a samar da kayan aiki da kuma isassun ma'aikatan jinya da ƙwararrun likitoci, da magunguna domin saukakawa talakawa, kasancewar suna taka muhimmiyar rawa wajan cigaban Demokaradiyya a jihar nan.

Har yanzu ranka ya dade! akwai bukatar kara yin waiwaye ta fuskar samar da tsaro, domin har yanzu akwai yankuna da dama da waɗannan bayin Allah ke cin karensu ba babbaka, muna fatan za a ci gaba da ɓullo da hanyoyi da dabarun da ya kamata domin dakile wannan sabga kwata-kwata, domin al'umma su samu sakewa da walwala, kasancewar zaman lafiya shine kashin bayan ci gaban kowace al'umma a duniya.


Zaman kashe wando a tsakanin matasa, wannan shima ya na daga cikin abubuwan dake kawo tarnaki, Ranka ya dade ta wannan fuskar, yana da kyau a samar da wani tsari mai sauƙi wanda za a riƙa koyawa matasa sana'o'in hannu domin dogaro da kai, wannan zai taimaka wajan rage masu zaman kashe wando a tsakanin al'umma musamman matasa, waɗanda basu samu damar yin ilimin zamani ba.


Haka Mai girma gwamna a dubi hanyoyin karkara wadanda ke matukar bukatar gyara, kasancewar akwai manyan kasuwanni, inda manyan motoci ya kamata su shiga domin dauko kaya ko saukewa amma basu samun damar zuwa wadannan wurare saboda rashin kyawun hanya, idan aka dubi wadannan hanyoyi aka gyara, sannan aka kirkira sabbi, wannan ma zai taimaka wajan farfado da kasuwanci a jihar Zamfara, kasancewar Allah ya sanya albarka a cikin kasuwanci.

A ɓangaren ilimi, kasancewar ilimi shine babban jigo, kuma babban bango wanda ake jingina da shi, wajan kaiwa ga kowane irin ci gaba, Ranka ya dade! har yanzu akwai 'ya'yan talakawa masu bukatar ganin sun samu ilimi mai inganci, to sai dai rashin karfin iyayensu na daukar nauyin karatunsu ne ya sanya sun ka koma 'yan kallo ta wannan gyafen, akwai bukatar fitar da wani tsari wanda zai binciki wadannan mutane domin taimaka masu ta kowane fanni, domin ganin sun samu ilimi mai inganci wanda zai taimaki rayuwasu, da al'umma baki ɗaya.


Ruwa sune rayuwa; Ranka ya dade Sir, a cikin girmamawa! Nake kara tuni, akwai yankuna dama a jihar ta Zamfara da har yanzu ruwa basu wadacesu ba, daga ciki har da babban birnin jihar wato Gusau, inda da zarar an samu kwana biyu ba a kawo ruwan fanfo ba, duk inda ka kyallara idanunka gungun mutane za kayi tozali da su suna jerin gwanon neman ruwa ido rufe, mata da maza, yara da manya. Ranka ya dade! muna cike da burin ganin wannan matsala ta ruwan sha ta zama tarihi a jihar Zamfara baki daya.

Rayuwa sai da abinci; Mai girma gwamna! Kasancewar kaso mai yawa na al'ummar jihar Zamfara manoma ne, kuma sun dogara ne kacokan wajan aiki gona, domin wadata jiha da ƙasa, da abinci, kuma damina na ci gaba da kankama. Ranka ya daɗe Sir! Akwai amfani sosai a dubi matsalar manoma, a kan abin da yafi ci musu tuwo a kwarya, domin share masu hawayensu, don ganin jihar nan ta samu tsayuwa da ƙafafunta wajan ciyar da kanta da abinci.


Ranka ya dade! akwai abubuwa da dama da lokaci ba zai iya bani damar zayyana su ba, amma a karo na gaba zanyi magana a kansu insha Allahu. Amma idan muka kwatanta irin ayyukanka na shekara daya zamu iya maka shedar zama zakaran gwajin dafi a tsakanin gwamnoni wadanda kuke gudanar da mulki a lokaci daya da su.

Nan nake son in dan dasa aya, tare da addu'ar Allah yasa wannan rubutu nawa, zaiyi tozali ga idanun mai girma gwamna, kuma inyi kira ga sauran gwamnonin kasar nan da zuyi koyi da kai, da kuma irin ayyukanka, domin ganin kasar nan ta ci gaba ta kowane ɓangare.

A karshe ina yi maka fatan alheri tare da addu'ar samun kowace irin nasara a cikin gwamnatinka, Allah ya maka kariya ga masu son ganin gazawarka, Allah ya maka jagora kar ya barka da dabararka.

Allah ya bamu lafiya da zama lafiya a jihar Zamfara da arewa da  Najeriya dama duniya baki daya.

Daga naka mai son ganin ci gaban jiharka ta Zamfara, kuma wanda yake a karkashin ikonka.

Nura Muhammad Mai Apple, Shugaban Kungiyar Matasa 'yan Gwagwarmaya 08133376020


Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Masana sun ce daga cikin abubuwan da suka sa dan Adam yin galaba a kan sauran halittu shi ne yadda yake iya hada kai. Don mutum shi kadai ba zai iya gwada karfi da zaki ko giwa ba. Amma idan ya hada karfi da sauran ‘yan uwansa babu kalubalen da ba za su iya tinkara ba. Hadin kai kuma ba ya tabbata sai da yarda, kuma yarda sai da mu’amala. Masu hikimar magana sun ce, Allah Ya halicce mu da kunne biyu, ido biyu amma sai ya yi mu da baki daya domin mu kalla, mu kuma saurara fiye da yadda muke magana.  Amma sai ya kasance cewa mun fi son yin magana fiye da saurare. Sau da yawa idan muna tattaunawa da wadansu ba ma mayar da hankali kan abin da ake fadi. Kawai jira muke mutum ya kai aya - idan ba mu katse shi ba kenan, domin mu fadi namu ra’ayin. Ga shi kuma ba mu son jin ra’ayoyin da suka sha bamban da namu. To ina za a samu fahimtar juna har a yi aiki tare?  Babu wanda rayuwarsa iri ɗaya da ta wani, kowa da irin  jarabawar shi,  kowa kuma da irin ta shi f...

Coronavirus; Me kuke so ku sani kan matakan kariya daga cutar Covid19

Wadan ne abubuwa ne kuke so ku sani, sannan wadanne matakan kariya kuke so ku sani kan wannan cuta  Ya  gwamnatin Najeriya ta hana mutane baki shiga da fita a kasar nan sannan gwamnati ta fara gudanar da bincike domin gano ko akwai mutanen da suka kamu da cutar a dalilin yin mu’amula da dan kasar Italy a jihohin Legas da Ondo. Daga nan hukumar hana yaduwar cututtuka ta yi kira ga mutane da su kiyaye hanyoyin samun kariya daga kamuwa da cutar da hukumar ta bada. HANYOYIN SAMUN KARIYA DAGA CUTAR: 1. Yawaita wanke hannu da ruwa da sabullu ko kuma da man tsaftace hannu ‘Hand Sanitizer’ idan babu ruwa. 2. A rika tsaftace muhalli. 3. Idan za a yi tari ko kuma atishawa a yi amfani da tsumma domin kare baki da hanci. 4. A guji yawan kusantan mai fama da mura ko kuma alamomin cutar. 5. Wurarren aiki su tabbatar sun ajiye ruwa da sabullu domin ma’aikata su rika wannke hannu ko kuma a ajiye man tsaftace hannu. 6. A guji shan magani ba tare da izinin likita ba. ...

Pakistani Campaigner for the ‘Disappeared’ Himself Goes Missing Four Activists Feared Forcibly Disappeared in Sindh Province

Pakistani Campaigner for the ‘Disappeared’ Himself Goes Missing Four Activists Feared Forcibly Disappeared in Sindh Province Saroop Ijaz It was only last month when Punhal Sario marched from the Pakistani cities of Hyderabad to Karachi to demand the return of fellow activists who had gone “missing,” a Pakistani euphemism for those forcibly disappeared by the state authorities. Now, Sario himself is feared missing . Witnesses say that Sario, a 58-year-old human rights activist and head of the Voice for Missing Persons of Sindh, was abducted from Hyderabad by security forces on August 3. Four days later, men in plainclothes accompanied by police officials abducted three other people – Partab Shivani, a teacher and activist; Naseer Kumbhar, a writer; and Mohammad Umer, a political party worker – from the Tharparkar district of Sindh province. Pakistani authorities deny any involvement, but have produced no information on the men’s whereabouts. In a further show of intimidation of cri...