Skip to main content

Posts

KUNGIYAR YAZEED NETWORK TA KARBI KUNGIYOYIN MATA 7

wasu daga cikin kungiyoyin mata                     ceo founder Yazeed Network Yazeed Network kungiya ce da aka assasa kuma aka bude ta domin tafiya kafada-da-kafada da sauran kungiyoyin dake fafutikar ilmantar da al'umma, hadi da wayar da kan al'umma akan manufofi hadi da bayyana alherai na (Alh Yazeed Shehu Danfulani Mai Doya), wadanda yake yi ga al'umma. Wata jigo daga cikin babbar kungiyar Yazeed Trust Fund ce ta kirkiri kungiyar, domin hada karfi da karfe, wajan wannan gwagwarmaya. Hajiya Aliya Saraki, ita ce shugabar Kungiyar Yazeed Network. A kokarin kungiyar na ganin ta zakulo kungiyoyin mata a sassa daban-daban na jihar Zamfara, a Ranar alhamis din da ta gabata ta karbi wasu gungun kungiyoyin mata 7 wadanda suka jaddada goyon bayansu ga tafiyar (Alh Yazeed Shehu Danfulani Garkuwan Matasan Gusau Lamidon Tsafe). Jawabin shugabar kungiyar a yayin taron ta jinjina wa tawagar wadannan kungiyoyi tare da shan alwas...

SHUGABAR YAZEED NETWORK TA KARBI TAWAGAR MANYAN KUNGIYOYIN MATA DOMIN NUNA GOYON BAYA WAJAN CI GABAN AL'UMMA

Kungiyar Yazeed Network wanda Hajiya Aliya Saraki ke shugabanta, ta karbi tawagar wasu ayarin kungiyoyin Mata domin marawa tafiyar (Alh  Yazeed Shehu Danfulani baya, wannan karbar na zuwa  ne a daidai lokacin da ayyukan alheri ke ci gaba da sauka a cikin al'umma ta hannun Alh Yazeed Shehu Danfulani, Wadannan kungiyoyi sunyi la'akari da muhimmancin dake akwai wajan irin amfanin al'umma, musamman zuwa ga marasa galihu masu kokarin ganin sun dogara da kansu, a lokacin karbar wannan tawagar an gudanar da jawabai da dama mabambanta wasu daga cikinsu shine, shuwagabannin wadannan kungiyoyi sun nuna farin cikinsu  matuka da gaske a kan irin yadda wannan bawan Allah ya himmatu wajan ganin marayu da marasa karfi sun amfana a cikin arzikin da Allah yayi masa. A lokacin jawabin godiya wanda shugabar wannan kungiya ta Yazeed Network Hajiya Aliya saraki tayi matukar nuna farin cikinta a bisa wannan dogon nazari da wadannan bayin Allah su kayi wajan zuwa a hada han...

Shekara Daya; Hon Kabiru Amadu Mai Palace A Sikelin Nazari.

Assalamu alaikum ranka da ya dade barka da warhaka da fatan kana cikin koshin lafiya, ina amfani da wannan dama domin taya ka murnar cika shekara daya a kan jan ragamar jagorancin kananan hukumomin Gusau da Tsafe a majalisar wakilai, mataki na kasa, Allah ya kara  kyakkyawan jagoranci, amin! Ko shakka babu, zamanka a saman wannan kujerar a Gusau da Tsafe wani babban abun nasara ne, kuma abun sam barka ne, idan muka kalli yadda kake gudanar da wannan wakilci a babban birnin tarayyar Kasa. Falsafa da kuma irin tanadi na Demokaradiyya wadda itace adon dan kasa, zamu iya cewa ka taka muhimmiyar rawa wajan ganin ka kashe zaman kashe wando a tsakanin matasa. Wani babban abun sha'awa shi ne; idan muka kalli yadda mutane ke cin gajiyar wakilcinka, zamu iya cewa abun farin ciki ne da jin dadi. Rayuwa; a kowane lokaci babban abun da talaka ke bukata wajan masu rike da madafun iko, shi ne; samar masa da ingantacciyar rayuwa, kama tun daga, lafiya, ilimi, tsaro, ruwan sha, da kum...

Cikar Shekara Daya; Gwamna Matawalle a Sikelin Nazari!

Assalamu alaikum, Ranka ya dade barka da warhaka da fatan ana ci gaba da gudanar da mulkin wannan jiha cikin koshin lafiya. Allah ya sa haka. Ranka ya dade Sir, cike da girmamawa nake ta ya ka murnar cikarka shekara daya a kan karagar jagorancin al'ummar jihar Zamfara, ko shakka babu wannan babban abun farin ciki ne da sambarka. Allah ya maka jagora har zuwan wa'adin mulkinka. Ranka ya dade Sir! A nazarce kwanaki 360 da ka share kana jan ragamar jihar nan, ko shakka babu an samu cigaba a wurare da dama, kuma abun Yabawa ne a bisa wannan. Mu mun san cewa; ko da  Allah madaukakin sarki ya baka jagorancin wannan jihar ka sameta ne a hargitse, cikin wani mummunan yanayi marar dadi, musamman ta fuskar tsaro, wanda a lokacin mutumin jihar Zamfara a kullum cikin fargaba yake sakamakon mummunan ta'adin 'yan ta'adda, wadanda suka yi sanadiyar rasa rayukan dubban mutune, hadi da cilastawa dubban mutane barin muhallansu ba cikin shiri ba. Hakika abun sambarka ne, ...

Barka Da Ranar Yara Ta Duniya

kowace shekara majalisar dunkin duniya na ware 27 ga watan 5 domin murnar zagayowar samun 'yancin yara, wannan na zuwa ne la'akari da muhimmancin dake akwai da kuma irin  yadda ya kamata a kula da yara, kasancewar wata rana sune manyan gobe. Ranar ta bana na zawa ne a lokacin da duniya ke cikin firgita da gigitar halin da ta tsintsin kanta a ciki na mummunar annobar cutar korona, a wannan shekarar bukin ba zai samu wani armashi ba, kasancewar har yanzu duniya bata murmure ba akan cutar covid19, wanda ya hallaka dubban mutane a sassa daban-daban na duniya. Ita ma Najeriya ta kan bi sahun takwarorinta wajan gudanar da irin wannan biki a duk shekara, sai dai bana wannan biki ba zai yiyuwa ba, kasancewar wasu daga cikin jihohin ƙasar suna fama da dokar kulle domin kandagarkin hana yaɗuwar cutar korona. Bikin yana tara makarantu da dama inda manyan mutane musamman ma'aikatan gwamnati suke halarta domin kallon faretin girma, inda wasu lokutan akan aza gasa kuma a gabata...

Rayuwa; me nene mararrabar Talaka da bawa a yau

idan muka yi tsinkaye muka bibiyi tarihi da kuma yadda rayuwar bayi ta kasance a shekaru da dama da suka gabata, zamu ga sun sha fama ba kaɗan ba, ta kowane fanni na rayuwa domin ana fataucin mutune kamar yadda mafarauta ke farautar dabbobin daji. Ana kama mutane daga wannan gari zuwa wancen, daga wannan kasa zuwa waccen, domin kaiwa a siyar, kuma aka dauki wannan a matsayin sana'a. A wancen lokaci, idan ka siyo bawa a kasuwa, ya zama mamanlakinka, zaka kaishi a gidanka ne, ko gonarka koma duk inda kake bukatarsa domin yayi maka ayyukan da kake so, ko ya so ko bai so ba, wannan cilas ne a wuyansa. To sai dai duk da haka, shi kuma mamalakin bawan ya zama wajibi a kansa cin sa da shansa kula da lafiyarsa da kuma wajan kwanansa, da tsare masa dukkanin bukatun yau da kullum. Idan masu karatu zasu yi dogon nazari a kan wannan shimfidar zasu fahimce inda na dosa ko da kuwa ban iyar da furta abun da nake son furtawa ba. Idan muka kalli yadda bayi a lokacin mulkin mallaka sun ...

Dokar Kulle; Jinjina ga gwamnatin Jihar Zamfara

tun bayan samun bullar cutar nan mai sarke numfashi ta Covid-19 a jihar Zamfara. A kokarin gwamna Bello Muhammad Mawatallen Maradun, na ganin ya dakile yaduwar cutar a cikin jihar tasa, yake ta shige da ficen ganin gwamman mutane basu harbu da cutara a jihar ba. Gwamna Matawallen ya bullo da wasu sabbin tsare-tsare daga ciki har da jan hankulan al'umma wajan rage tarurukan jama'a barkatai, da kuma bayar da tazara tsakanin mutum da mutum, hadi da samar da sabulun tsaftacce hannuwa, da kuma samar da kayayyakin feshi, wanda alhamdulillahi mun sheda haka, tun lokacin da aka samar da wadannan kayan aiki, mun shedi an nada wani kwamiti mai karfin gaske, wanda ya bazama lunguna da sakuna, ma'aikatai da kuma bankuna, da unguwanni a na gudanar da aikin feshi domin kandagarkin bazuwar annobar cutar Korona mai saurin yaduwa kamar wutar daji. Haka mun shedi irin yadda muka ga an samar da wasu mashuna masu kafa ukku, na daukar marasa lafiya, ga duk wanda aka ga ya nuna alamun ka...