Barka Da Ranar Yara Ta Duniya



kowace shekara majalisar dunkin duniya na ware 27 ga watan 5 domin murnar zagayowar samun 'yancin yara, wannan na zuwa ne la'akari da muhimmancin dake akwai da kuma irin  yadda ya kamata a kula da yara, kasancewar wata rana sune manyan gobe.

Ranar ta bana na zawa ne a lokacin da duniya ke cikin firgita da gigitar halin da ta tsintsin kanta a ciki na mummunar annobar cutar korona, a wannan shekarar bukin ba zai samu wani armashi ba, kasancewar har yanzu duniya bata murmure ba akan cutar covid19, wanda ya hallaka dubban mutane a sassa daban-daban na duniya.

Ita ma Najeriya ta kan bi sahun takwarorinta wajan gudanar da irin wannan biki a duk shekara, sai dai bana wannan biki ba zai yiyuwa ba, kasancewar wasu daga cikin jihohin ƙasar suna fama da dokar kulle domin kandagarkin hana yaɗuwar cutar korona.

Bikin yana tara makarantu da dama inda manyan mutane musamman ma'aikatan gwamnati suke halarta domin kallon faretin girma, inda wasu lokutan akan aza gasa kuma a gabatar da kyaututuka ga makarantun da suka cinye gasar.

A bisa wannan muke ƙara kira ga gwamnatin Najeriya da kuma na jihohin kasar nan da su kara matsa kaini wajan ganin sun magance wannan annoba, a cikin ƙasar baki daya.

Daga Nura Mai Apple

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’